Taron jam′iyyar SPD ta Jamus | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron jam'iyyar SPD ta Jamus

Jam'iyyar SPD da ke cikin gwamnatin hadaka ta Jamus ta sake zaben Sigmar Gabriel a matsayin shugabanta.

Shugaban jam'iyyar SPD ta Jamus Sigmar Gabriel ya yi tazarce

Shugaban jam'iyyar SPD ta Jamus Sigmar Gabriel ya yi tazarce

Gabriel dai shi ne mataimakin shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel kuma minstan tatalin arziki na kasar. Jam'iyyar ta SPD ta sake zabensa ne a yayin taronta na shekara-shekara a Berlin babban birnin kasar. A yayin taron dai Gabriel ya zargi shugabar gwamnatin Jamus din ta jam'iyyar CDU Angela Merkel da yin fuska biyu a kan batun 'yan gudun hijira da ma kuma tsaurara matakan tsuke bakin aljihu a nahiyar Turai wanda ya ce hakan ne ya bai wa jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta kasar Farasan wato National Front damar samun nasara a zaben gundumomin da ya gudana a karshen mako. Dama dai Merkel na fuskantar matsin lamba daga bangarori da dama ciki kuwa har da jam'iyyarta ta CDU dangane da matakan da take dauka kan batun 'yan gudun hijira da ke kwararowa nahiyar Turai.