Taron jamiyyar adawa ta NLD a Birma | Labarai | DW | 08.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron jamiyyar adawa ta NLD a Birma

Jamiyyar adawa ta Aung San Suu Kyi a Birma ta ƙaddamar da taron ƙoli dan gudanar da shirye-shiryen da take buƙata wajen tinkarar zaɓen 2015

ARCHIV -Die birmanische Friedensnobelpeisträgerin und Führerin der Oppositionspartei NLD, Aung San Suu Kyi, bei einer Ansprache in Rangun am 02.02.2013. Mit dem Ende der Militärherrschaft 2011 hat der demokratische Aufbruch begonnen. Jetzt muss die Lady im eigenen Hause aufräumen: Erstmals seit der Gründung vor 25 Jahren findet jetzt ein Parteitag statt (8.-10. März). Es werden mehr als 800 Parteimitglieder aus dem ganzen Land in Rangun erwartet. EPA/LYNN BO BO (Zu dpa-Korr.: «Erstmals Parteitag der NLD - Birmas Opposition braucht frischen Wind» vom 07.03.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++

Aung San Suu Kyi

Jamiyyar adawar Birma ta Aung San Suu kyi ta buɗe taron ƙolin ta mai cike da tarihi wanda ake ganinsa a matsayin wata dama na bunƙasa jamiyyar wadda duk da cewa tana da farin jini, bata gama ƙwarewa a fagen siyasa ba, kuma a yanzu haka tana fuskantar ƙalubale a cikin gida gabannin babban zaɓen ƙasar da ake sa ran yi a shekarar 2015 idan Allah ya kai mu.

To sai dai masana sun fara sanya alamar tambaya kan ko jamiyyar ta NLD na da ƙarfin tinkarar irin ƙarin ƙalubalen da zata fuskanta wajen tsayawa takara a wannan ƙasar da ke fama da koma bayan tattalin arziƙi wacce kuma kusan duk cibiyoyin samar da abubuwan more rayuwarta sun durƙushe.

Aƙalla wakilai 850 ke halartar wannan taron na wuni uku wanda zai gudanar da sauye-sauye a tsarin shugabancin jamiyyar ya kuma tsara irin matakan da zata ɗauka nan gaba musamman wajen cimma burinta na karɓar ragamar mulkin ƙasar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar