1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya

March 6, 2014

Jam'iyyar APC a Najeriya ta bayyana muhimman manufofin da za ta sanya a gaba a babban taronta wanda ke zama irinsa na farko da ta gudanar a Abuja gabannin zabukan 2015.

https://p.dw.com/p/1BLRa
Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Babban taron dai ya kasance damar farko da shugabanin jam'iyyar APC na riko suka samu na bayyana dalilin kafa ta da ma manufofin da ta sanya a gaba da suke ganin za su iya kai su tudun na tsira a fafatawa da suke shirin yi da jam'iyyar da ke mulki ta PDP.

An dai yi jawabai da suka tsuma 'ya'yan jam'iyyar ta APC har ma da sanya su rawar kafa kama daga batun kamanta adalci a mulki da yaki da cin hanci da rashawa da ma bukatar samar da tsaro da ke zama muhimman manufofin da duka manyan jam'iyyar suka rattaba hannu a abin da suka kira alkawari a tsakaninsu da al'ummar kasar.

Gwaman Jihar Edo Adams Oshimole na cikin wadanda aka rinka yiuwa tafi a jawabin da ya yi, inda ya ke cewa ''dukaninmu nan masu gwagwarmaya ne na samar da canji a Najeriya domin kaucewa yanayi na rashin tabbas don jagorantar kasar da mutane da dama ke son ficewa daga cikinta zuwa wacce suke son dawowa''.

Wahl Nigeria Proteste
Jiga-jigan APC na son ganin rauywar talaka a Najeriya ta inganta.Hoto: DW/U.Abubakar Idris

Wannan taro na jamiyyar ta APC da ya samu hallartar daukacin gwamnonin jamiyyar 16 a yanayin da ke nuna jan damara da suka yi domin tunkarar zaben 2015 inda za su faffata da jamiyyar PDP, Ko wane kwarin gwiwa suke da shi ga manufofin jamiyyar? Alhaji Tanko Umar Almakurra shi ne gwamman jihar Nasarawa.

''Mun tabbatar da irin aiyyukan da ta sa gaba da irin akidarta da irin abubuwan da za ta yiwa jama'ar Najeriya, wadannan sun shafi kowane irin abubuwa da za su taimakawa rayuwar jama'a musamman talakawa, shi aka zauna aka tsara domin a gwada a ga yadda wadansu siyasu suka yi a baya da abinda jamiyyar APC za ta yi''

Ko da ya ke manyan shugaban jamiyyar ta APC sun kasance cike da murnar yadda suke ganin tafiyar ta su a gamayar jam'iyyar adawar wacce ita ce irinta ta farko a tarihin Najeriya, musamman jan layi a kan batun dan takarar shugaban kasa da suka amince a bari a gama gina jam'iyya, to ko wane kalubale ke gabansu a yanzu? Dr. Usman Bugaje jigo ne a jam'iyyar ta APC.

Ya ce ''akwai kalubale saboda fada ya na da sauki amma cikawa na da wahala don haka muna sane da cewa abubuwan da muka fada na jam'iyyar nan abubuwa ne manya da ke bukatar yunkuri da kuma bukatar kai zuciya nesa, a tsaya a dubi Allah a dubi Annabi da kuma talaka . Wannan kalubalen da ke gabanmu shi ne mu din nan da mu ke son mu yi haka to mu daure mu yaki zuciyarmu mu san cewa talakawa za su rike mu da wannan maganar, idan har mun yi hakan in kuma muka kasa za su san cewa mun kasa.''

Wahl Nigeria Proteste
Tsaro na daga cikin abubuwan da APC ke rajin tabbatarwa.Hoto: DW/U.Abubakar Idris

Duk da armashin da ake ganin taron ya yi , korafe-korafen da ake samu a matakin jihohi na zama abinda ke daga hankalin 'ya'yan jam'iyyar da dama a daidai lokacin da fagen siyasar Najeriyar ke kara daukar dumi musamman saboda zaben na 2015.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Muhammad Awal Balarabe/Ahmed Salisu