Taron G7 na fuskantar rudu | Labarai | DW | 08.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron G7 na fuskantar rudu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace sauran kasashe mambobin G7 ka iya cimma yarjejeniyar kasuwanci ko ba tare da kasar Amirka ba.

Yayin da shugabannin kasashe mafi karfin tattalin arziki da masana'antu a duniya wato G7 ke fara taro a kasar Kanada, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gragadi shugaban Amirka Donald Trump kan yunkurin haddasa rikicin cacar baka tsakanin mambobin kungiyar.

Macron ya bayyana haka ne bayan da shugaba Trump ya jaddada halartar taron domin kare muradun kasuwancin Amirka, taron na zama wata dama da zai ba wa shugabannin damar tattauna hanyoyin warware matsalar harajin shugaba Trump ya yi karafa da kasashen ke dillacinsu zuwa Amirka.

Sai dai barkewar cacar baka tsakanin saauran kasashe shida da Amirka gabannin fara taron, ya haifar da shakku kan tasirin da ake son taron ya cimma a tsakanin kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya da Kanada da kuma kasar Japan.