Taron G7 kan kasuwanci ya watse baram-baram | Labarai | DW | 03.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron G7 kan kasuwanci ya watse baram-baram

Taron Kungiyar G7 wanda kasashen Turai da Amirka suka shirya a Kanada da nufin shawo kan rikicin kasuwancin da ya hada kasashen ya kawo karshe ba tare da samun wata matsaya ba. 

Taron dai ya watse ne baram-baram ba tare da mahalarta sun iya fitar da wata sanarwar hadin gwiwa ta karshen zaman taro ba, inda duk bangarorin kowa ya gudanar da nashi taron manema labarai domin bayyana matsayinsa. 

Daga daya bangaren dai ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashen na Turai dai sun bayyana rashin amincewa da tsarin kasuwancin kasar ta Amirka inda suka yi kira ga Shugaba Donald Trump da ya yi watsi da matakinsa na dora haraji kan bakin karfe da kuma karfen sanholo 

Sai dai bangarorin biyu sun yi alkawarin sake haduwa a mako mai zuwa a birnin Quebec na Kanada domin sake tattauna wannan rikici na kasuwanci da ke kara kamari tsakanin kasashen na Turai da abokiyar huldar kasuwancinsu ta Amirka.