Taron EU kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 17.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron EU kan 'yan gudun hijira

A yayin da kungiyar tarayyar Turai ta fara taron ta a yau a birin Brussels matsalolin 'yan gudun hijira da da batun kawo sauyi da Birtaniya take neman yi a kungiyar na daga cikin batutuwan da zasu mamaye taron.

Taron zai kuma tattauna kan sake wai-wayar batun kwararar 'yan gudun hijira dake cigaba da addabar nahiyar tare da daukar matakan bai daya don warware matsalar.

Shugaban Hukumar tarayyar Turai Donald Tusk a yayin taron yayi nuni da cewar.

Kamar yadda nasha nana tawa a watanni da dama,daga farkon samun matsalar 'yan gudun hijira babu wata hanya ta daban, wanda yanzu nayi farin cikin yadda hukumar tayi na'am da kara daukar matakan kan iyakoki,don wannan matakin shine manufar dakile kwararar 'yan gudun hijira.

Kazalika taron zai kuma duba batun takunkumin da aka sanyawa Rasha kan rikicin kasar Ukrain.