Taron dangi a yaki da sauyin yanayi | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron dangi a yaki da sauyin yanayi

An fidda wani tsarin na yaki da sauyin yanayi a duniya wanda ake son cimma nan da shekara ta 2030

Shugabannin kasashen duniya da ke halartan taron kare mahalli na MDD a birnin New York na kasar Amirka, sun bukaci a fadada aiki da makamashin da ake sabontawa, kana suka amince da ware biliyoyin dalar Amirka domin tallafawa kasashe masu tasowa, don rage dumamar yanayi. Taron kolin wanda sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya shirya, an tsara shi don cimma buri nan da shekara ta 2030. Matakan da ake son cimma sun hada da rage sare dazuka kana da habaka samar da abinci. Shugabannin kasashen duniya sama da 120 suka halarci taron.