Taron birnin Vienna kan kasar Siriya bai cimma manufa ba | Labarai | DW | 17.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron birnin Vienna kan kasar Siriya bai cimma manufa ba

Mahalarta taron sun amince da karfafa hadin kai don samar da wani shirin tsagaita wuta da zai yi aiki sosai. Amma ba a sanya lokacin komawa teburin sulhu a Geneva ba.

Österreich Wien Syrien Friedensgespräche - Lawrow & Kerry

Lavrov da Kerry a birnin Vienna

A wannan Talatar manyan wakilan kungiyar nan ta kasa da kasa da ke tallafa wa kasar Siriya da suka yi wani taro a birnin Vienna sun amince da su yi kokarin samar da wani shirin tsagaita wuta da zai yi aiki a Siriya. Sai dai sun kasa zayyana hukuncin da za a yi wa duk wanda ya ki mutunta shirin tsagaita wutar. A taron manema labarai na hadin guiwa sakataren harokin wajen Amirka John Kerry ya ce karya ka'idojin tsagaita wutar abin damuwa ne.

"Ba wanda ya gamsu da halin da ake ciki a Siriya. Abin damuwa ne matuka yadda ake cigaba da karya shirin tsagaita wutar a kwanakin nan. Rasha da Amirka na aiki tare don karfafa guiwa bisa manufar samun mafita daga rikicin."

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov cewa ya yi.

"A jawabinsa Kerry ya ce Rasha da Iran na mara wa Assad baya, amma ba haka ba ne ,ba ma tallafa wa Assad, muna tallafa wa yakin da ake yi ne da ta'addanci. Yanzu haka dakarun gwamnatin Siriya ke da karfi a yakin duk da kura-kuran da ake yi."

A nasa bangare, wakili musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura ya kasa ba da lokacin da za a koma kan teburin sulhu da zai share fagen samun maslaha ta siyasa.