Taron Berlin kan Ukraine ya kasa cimma wata matsaya | Labarai | DW | 20.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Berlin kan Ukraine ya kasa cimma wata matsaya

Taron birnin Berlin kan sasanta rikicin Ukraine da ya gudana ranar Laraba da yamma ya kawo karshe da daukar alkawari kadai na samar da yarjejeniyar zaman lafiya a Ukraine nan zuwa karshen watan Nowamba. 

Taron koli kan batun rikicin kasar Ukraine da ya gudana a birnin Berlin ya kawo karshe da daukar alkawarin samar da yarjejeniyar zaman lafiya ta kawo karshen rikicin gabacin kasar ta Ukraine nan zuwa karshen watan Nowamba. 

Taron wanda ya samu halartar Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Ukraine Petro Poroshenko a karkashin jagorancin Jamus da Faransa na da burin sake farfado da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a birnin Minsk a watan Febrairun shekara ta 2015 wacce ta susuce yau kimanin wata daya. Sai dai Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa taron bai cimma wani abin a zo a gani ba.

Ta ce: "A yau ma dai kamar yadda ta kasance a baya babu wani abin a zo a gani da aka cimma, sai dai mun tattauna kan ayyukan da za mu yi a nan gaba kan sake farfado da shirin tsagaita wutar, amma a zahiri da akwai sauran jan aiki a gabanmu."

Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekara daya da Shugaba Putin na Rasha ya halarci wani taro kan batun shawo kan rikicin kasar Ukraine. Shugabannin kasashen hudu dai za su rubuta a nan gaba wani sabon jadawali na tsarin samar da zaman lafiyar kasar ta Ukraine wanda amma Shugaba Hollande na Faransa ya bayyana bukatar ganin ya kiyaye duk matakan da yarjejeniyar da aka cimma a baya a birnin Minsk ta tanada na tsagaita wuta da shirya zabe a yankin gabacin kasar ta Ukraine.