1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron bada agaji ga kasar Siriya

January 15, 2014

A wannan Larabar ce wakilan kasashen duniya ke gudanar taro don neman tallafi na kimanin dala biliyan shidda da rabi domin fuskantar halin da ake ciki a Siriya wadda yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/1Aqeb
Syrien Präsident Baschar al-Assad September 2013
Hoto: Reuters

Taron da kasar Kuwait ta karbi bakuncinsa dai shi ne taro na neman agaji mafi girma a tarihi, kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce matsanancin halin da aka shiga a kasar ne ya tilastawa kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya yanke shawarwar shirya taron don neman wannan tallafi.

Tuni dai wakilan kasashen duniya ciki har da na Amurka waddda ke kan gaba wajen tallafawa kasar ta Siriya da kuma hukumomin bada agaji na duniya suka isa Kuwait din tun a jiya Talata don gudanar da wannan taro, inda a hannu guda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da aniyarsa ta kara agaji na cimaka da ya ke bawa wadanda ke cikin hali na bukata a Siriyan.

Rikicin na Siriya dai ya zuwa yanzu ya hallaka mutane sama da dubu 130 wanda galibinsu fararren hula.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu