1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron AU kan Mali da Sudan da Sudan ta Kudu

October 25, 2012

Shugabar kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi kira ga kasashen Sudan da Sudan ta Kudu su gaggauta samun hanyoyin warware rikicin yankin Abiyei.

https://p.dw.com/p/16WC2
Hoto: picture-alliance/ dpa

Ya yin taron, wanda shi ne karo na 339, kuma aka yi shi birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha, shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini Zuma, ta ce lokaci ya yi da ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su kai ga warware matsalar yankin na Abiyei domin tantance wanda ya mallaki shi ko a samu zaman lafiya mai dorewa a tsakanin maƙotan biyu.

Baya ga wannan, Uwargida Dlamini Zuma ta yi kira musamman ga mahukunta Khartoum da su zage damtse wajen ganin sun warware rikicin arewacin ƙasar da ma dai yankin kudancin Kordofan da 'yan tawaye ke rike da shi.

Da ta juya kan rikicin Mali kuwa, shugabar ta ƙungiyar ta AU kira ta ce ta na da tabbacin cewar ƙoƙarin da su ke kan warware matsalar ƙasar zai kai ga nasara.

Tuareg-Truppen Mali
Karɓe arewacin Mali da 'yan tawayen su ka yi ya dagula tsaro a ƙasarHoto: picture alliance/Ferhat Bouda

'Ina da dukkan dalilan da su ka sa na gamsu cewar mastayar da mu ka cimma tare da tallafin kwamitin da mu ka kafa kan rikicin Mali da ma yankin Sahel zai taimaka wajen warware rikicin mali din cikin gaggawa'.

Game da tada ƙayar bayan da 'yan tawayen M23 na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo kuwa Dlamini Zuma ta yi kiran da a samar da wata taswirar zaman lafiya da za ta kai ga kawar da matsalar.

Yayin da shugabar ta AU ke wadanan kiraye-kiraye, muƙaddashin sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Jan Eliasson bada tabbacin ya yi na amincewar da kwamitin tsaro na Majalisar ta Ɗinki Duniya ya yi game da wani ƙuduri na wanzar da kawar da ƙalubale na tsaro a yankin yammacin Afrika.

Eröffnung der 21. Sitzung des UN-Menschenrechtsrats in Genf 2012
Majalisar Ɗinkin Duniya na ta ƙoƙarin kashe wutar rikicin MaliHoto: Getty Images

'Ya kyautu mu tallafa a samu gyara a siyasance da kuma amfani da karfin soji wajen magance matsalolin. Taron nan na Addis Ababa ya tattauna sosai game da game da yadda za a yi amfani da siyasa wajen cimma nasarar da aka sanya a gaba'.

Da ta ke sharhi game da waɗannan batutuwa da su ka danganci tashin hankali da su ka danganci Afrika ta yamma da kuma taron na kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya na AU, Florence Mpaaye da ke zaman ƙwararriya ta sha'anin tsaro a wata cibiya ta samar da zaman lafiya da ake Nairobin Kenya, cewa ta yi ya kyautu a sake zage damtse wajen kaiwa ga nasara.

'Ina jinjinawa ƙungiyar ta AU saboda kokarin da ta ke na cigaban Afrika da ma yunƙurin da ta ke na ganin an samu zaman lafiya da makoma kyakkyawa ga ƙasashen da ke Afrika to amma fa dole ne sai an sake zage damtse kan wannan batu kuma duk inda su ka yi abun yabawa to ya kamata mu jinjina mu su'.

To abin tambaya a nan ita ce shin ko ƙoƙarin kwamitin tsaron wanzar da zaman lafiya na kungiyar ta AU zai kai ga wanzar da zaman lafiya a Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Mali da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo? Lokaci ne kawai zai yi alkalanci.


Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu