Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Babban sakataren MDD ya gargadi shugabanni da ke halartar babban taro kan sauyin yanayi cewar, duniya na cikin wadi na tsaka mai wuya da ke bukatar daukar matakan gaggawa.
Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci kasashen da ke taro kan sauyin yanayi na COP27 da su daina yawan zargin juna da suke a kan matsalolin sauyin yanayi da ake ciki.
Kananan manoma na kasashen yankin Kudu da Saharar Afirka da na yankin kudancin Asiya wadanda ke fama da radadin tasirin sauyin yanayi, sun samu tallafin dalar Amirka biliyan daya da miliyan 400.
Shugabannin kasashen duniya masu yawa ne ke halartar taron sauyin yanayi da ke gudana a sanannen wurin shakatawan nan na Sharm el-Sheikh da ke a kasar Masar.
An karkare taron COP27 tare da cimma matsaya na ganin an taimaka wa kasashen da suka tafka asara a sakamakon matsalar sauyin yanayi da kudi.