Tarihin Sylvestre Ilunga sabon firaministan Kwango | Siyasa | DW | 21.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tarihin Sylvestre Ilunga sabon firaministan Kwango

Takaitaccen tarihin sabon Firaministan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Sylvestre Ilunga Ilunkamba wanda aka nada watanni hudu bayan zaben Shugaba Felix Tshisekedi kan karagar mulkin kasar.

Sabon Firaministan Sylvestre Ilunga Ilunkamba wanda dama ya rike mukaman minisotoci da dama tun shekarun 1980, ya fito ne daga kawancen jam'iyyun FCC da tsohon Shugaba Joseph Kabila ke jagoranta, kuma ya rike mukamin minista a lokuta da dama tun shekarun 1980 lokacin mulkin tsohon shugaba marigayi Mabutu Sese Seko. Sabon firaministan yana da jan aiki kan samar da matsaya tsakanin bangaren da ya fito na kawancen jam'iyyun FCC da kuma kawancen jam'iyyun CASH karkashin jagorancin Shugaba Felix Tshisekedi.

Ainahi Sylvestre Ilunga Ilunkamba ya fito daga tsohon yankin Katanga na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, dan shekaru 73 da haihuwa ya taba rike mukamun babban daraktan kamfanin jiragen kasa na kasa, gami da jagorancin kwamitin samar da sauye-sauye a kamfanonin gwamnati. Fiye da shekaru 40 Sylvestre Ilunga Ilunkamba ya shafe a harkokin siyasa. Ya ba da shawara ga tsohon shugaba marigayi Mabutu Sese Seko da zama minista cikin gwamnatin tsakanin shekarar 1980 zuwa da 1987. Sabon firaministan ya kasance kusa a cikin jam'iyyar da tsohon Shugaba Joseph Kabila ke jagoranci. Pius Muabilu dan majalisar dokoki kana mamba a kawancen jam'iyyun FCC ya ce sabon firaminista mutum ne mai hada kan mutane:


"Mutum ne wanda yake da kwarewa kuma yanzu ya dace za a gani yana aiwatar da ayyukan da ya kware a kai. Ba mutum ba ne mai wasa da hankalin jama'a, abin da na yarda shi ne mutum ne kwararre."

Jagorancin Sylvestre Ilunga Ilunkamba na kwana-kwanan nan ya kasance a kamfanin jiragen kasa lokacin da kamfanin ya fuskanci durkushewar tattalin arziki, amma 'yan adawa na ganin babu rawar da sabon firaministan zai tabuka wajen farfado da tattalin arzikin Jamhuriyar Dimukurydiyyar Kwango, kamar yadda wani jigo a kawance 'yan adawa na Lamuka mai suna Yves Kitumba a bangaren Kinshasa ke cewa:

"A ganin kawance Lamuka wannan nadin ba wani abu mai tasiri ba ne, saboda ci gaba na mulkin kawancen jam'iyyun FCC, da ke ci gaba da gudanar da jagoranci na wacaka. Idan za a tuna Ilunga babu abin da ya tabuka lokacin da ya jagoranci kamfanin jiragen kasa na kasar, kan ya karya kamfanin gwamnati da ya jagoranci sake musu sauye-sauye."

Akwai masu sharhi da ke ganin sabon Firaminista Sylvestre Ilunga Ilunkamba a matsayin tsauni tsakanin Shugaba Felix Tshisekedi da kuma mutumin da ya gada Joseph Kabila. Wani babban kalubale da ke gaban sabon firaministan na zama raba mukamai saboda yawan jam'iyyun da ke cikin kawance masu rinjaye a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.