1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin sabon firaminitan Tunisiya

December 16, 2013

Sabon firaministan Tunisiya Mehdi Jomaa mai shekaru 51 ya fara fuskantar kalubale daga bangaren adawan kasar da ya zargeshi da rashin sanin makaman aiki.

https://p.dw.com/p/1AaIt
Neuer Premierminister von Tunesien Mehdi Jomaa
Hoto: picture-alliance/AP Photo

An haifi Mehdi Joma'a kimanin shekaru hamsin da daya da suka gabata kuma ya gudanar da karatunsa baki daya a kasar ta Tunisia inda ya kammala a masatyin Injiniya. Ya gudanar da aiyyukansa a kamfanoni daban-daban na kasa da kasa masu zaman kansu wanda suka hada da Total da Hutchinson inda ya kasance shugaban kamfanin kafin ya yi murabus bayan da aka bashi mukamin minista.

Sabon firaministan na Tunisiya dai za a iya cewa farin shiga ne a harkokin siyasa hasalima ya tsunduma cikinta ne a watan Maris din da ya gabata, abinda shi kansa ya amince da shi sai dai ya ce bayan dan kankanin lokaci ya na da yakinin cewar lamura za su daidaita.

Ya ce ''ni kaina na san farin shiga ne ni a harkoki na siyasa, hasalima kamar kutse na yi mata. Wannan shi ne irin abinda juyin-juya hali ke jawowa. Ku dan bani lokaci domin duba lamuran kafin na ce komai kansu.''

kalubalen da Mehdi zai fuskanta

To sai dai duk da wannan rashin kwarewa ta tunkarar harkokin siyasa musamman ma dai wadda fagenta ke cike da rikici, Rached Ghannouchi guda daga cikin masu fashin baki na siyasar Tunisiya kuma a shugaban jam'iyyar Ennahada na ganin cewar Mr. Jomaa mutum ne da ya ke ganin zai iya rike wannan matsayi da aka bashi yadda ya kamata.

Rached Ghannouchi, Leiter Ennahda Partei Tunesien
Rached Ghannouchi shugaban jam'iyyar EnnahadaHoto: AP/dapd

Ya ce ''muna da tabbacin cewar wannan alama ce kyakkyawa kuma muna kan godabe mikakke da yardar Allah.''

A hannu guda kuma sauran 'yan siyasar kasar musamman ma dai wanda ke adawa da kawance jam'iyyun da Ennahada ke jagoranta na ganin wannan nadi da aka yi abu ne da bai dace ba kamar yadda Issan Chebbi na guda daga cikin jam'iyyun da ke adawa da Ennahada ke da'awa, inda ya kara da cewar Jomaa ba zai kasance shugaban da zai dama da kowa ba.

Shi ma dai Hamma Hammami na jam'iyyar Wokers Communist Party da ke adawa ya ce zai yi wuya ta sauya zani kasancewar Jomaa na matsayin guda daga ministocin gwamnatin baya.

Hamma Hammami
Hamma Hammami, guda daga ciki 'yan adawaHoto: picture-alliance/dpa

Ya ce ''Mehdi Jomaa mamba ne na gwamnatin da ta shude saboda haka ko ba dan jam'iyyar Ennahada ba ne shi babu wani sauyi da muke tsamanin gani.''

Matsalar rashin aikin yi a Tunisiya

Baya ga wannan kalubale da Mehdi Jomaa za fuskanta daga 'yan siyasar Tunisiya na rashin amincewa da shi a mastayin wanda suke ganin zai dama da kowa da ma kawo karshen irin kalubalen da kasar ta ke fuskanta, a hannu guda manazarta na ganin cewar sabon firaministan zai fuskanci dumbin matsaloli da suka da na tsaro da rashin aikin yi da matsala ta tattalin arziki.

Wani abu kuma da zai kasance kalubale ga sabon firaministan Tunisiyan shi ne batun girka sabuwar gwamnati wadda yake da makonni biyu kacal ya kafa, inda tuni jama'ar kasar suka fara sanya idanu don ganin irin mutane da sabuwar gwamnatin da za ta jagoranci kasar za ta kunsa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe