Tarihin sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson | Amsoshin takardunku | DW | 05.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin sabon Firaministan Birtaniya Boris Johnson

Bayan murabus din Firaminista Theresa May, Boris Johnson ya tsaya takarar neman shugabancin jam'iyyar Conservative, zaben da kuma ya lashe da kuri'u sama da kaso 66 cikin 100. Lamarin da ya ba shi damar zamowa sabon Firaministan Birtaniya a ranar 23 ga watan Yulin 2019.

Saurari sauti 06:02

An haifi Boris Johnson da ake yi wa lakabin Bojo a ranar daya ga watan Yunin 1964 a birnin New York na kasar Amirka. Mahaifinsa Stanley Johnson wanda babban dan siyasa ne da ya taba rike mukamin dan majalisar Birtaniya da kuma Turai, da mahaifiyarsa Charlotte Johnson Wahl dukkaninsu 'yan Birtaniya ne. Amma iyayen nasa sun koma Amirka da zama. Wannan ce ta sanya bayan haihuwarsa Boris Johnson ya samu takardar dan kasa biyu wato Amirka da kuma Birtaniya.

Asalin kakannin Boris Johnson na wajen uba Turkawa ne, ta hanyar kakansa Osman Kemal da kuma kakan kakansa Ali Kemal shahararren dan jarida kana ministan cikin gida a gwamnatin karshe ta Daular Turkiyya a shekara ta 1909. Asalin kakanninsa na wajen uwa Yahudawa ne Alias Avery Lowe da Helen Tracy Lowe-Porter. Amma shi yanzu yana bin darikar Anglikan ne na addinin kirista.

Bayan murabus din Firaminista Theresa May, Boris Johnson ya tsaya takarar neman shugabancin jam'iyyarsa ta Conservative, a bisa alkawarin aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga cikin EU a ranar 31 ga watan Oktoba, ko da yarjejeniya ko babu. Zaben da kuma ya lashe da  kuri'u sama da kaso 66 cikin 100 na 'ya'yan jam'iyyar. Lamarin da ya ba shi damar zamowa sabon Firaministan Birtaniya a ranar 23 ga watan Yulin 2019.

To sai dai kafin kai wa ga wannan mukami tun a shekara ta 2016 Boris Jonhson ya dauki matakin yin watsi da takardarsa ta dan kasar Amirka domin rike ta Birtaniya kadai.