Tarihin rayuwar Gareth Bale | Amsoshin takardunku | DW | 17.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin rayuwar Gareth Bale

An haifi Gareth Frank Bale a birnin Cardiff na yankin Wales da ke Burtaniya ranar 16 ga watan Yulin shekara ta 1989 kuma a Wales din ne ya yi karatunsa.

Tun Bale na karamin yaro dai ya fara nuna sha'awarsa ta wasannin motsa jiki sai dai lokacin da ya shekara tara da haihuwa ne ya fara wasan kwallon kafa gadan-gadan da wata kungiyar kwallon kafa ta Cardiff Civil Service Football Club.

Lokacin da ya cika shekara sha shidda da haihuwa ne ya fara takawa kungiyar kwallon kafa ta Southampton da ke Ingila leda cikin shekara ta 2006, kuma ya kasance dan wasa na biyu da ya fi kowanne dan wasa kankantar shekaru, kuma ya ci kwallonsa ta farko a club din ne ranar shidda ga watan Agustan wannan shekara a wani wasa da suka yi da kulab din Derby County.

Bayan da ya shekara guda a kulab din Southampton, inda ya samu buga wasanni arba'in da biyar gami da zura kwallaye biyar, Gareth Bale ya sauya sheka zuwa Totenham Hotspur kan wata kwantragi ta tsawon shekaru hudu a kan tsabar kudi fam din Ingila miliyan biyar, inda daga bisani aka kara kudi kan kwantragin nasa zuwa fam miliyan goma saboda kwazon da ya nuna.

Haka dai Bale ya cigaba da wasansa na kwallon kafa a Ingila inda ya samu jerin nasarori da suka sanya shi ya yi fice sai dai a farkon watan da ya gabata ne ya sake sauya sheka zuwa kulab din Real Madrid da ke Spain inda ya sanya hannu kan wata kwantragi ta tsawon shekaru shidda kan kudi kimanin euro miliyan dari.

Wannan sabuwar kwantragi da Bale din ya rattabawa hannu dai ta sanya shi yanzu haka ya kasance dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya duba da yawan kudin da za a bashi.

To baya ga wasannin da Gareth Frank Bale ya yi a kulabluka, a hannu guda ya bugawa kasarsa Wales wasa kuma ya fara hakan ne cikin shekara ta 2006 lokacin da ya kasarsa ta yi wani wasa da kasar Trinidad and Tabago. Bale dai ya kasance dan wasan da ya fi kowanne kankantar shekaru da ya taba bugawa Wales kwallo.

A bangaren iyali kuwa, dan wasan na da abokiyar zama mai suna Emma Rhys-Jones wadda budurwarsa ce tun suna makaranta kuma a ranar ashirin da daya ga watan Oktoban bara ne Allah ya basu haihuwa ta da namiji wanda suka radawa suna Alba Violet.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal