Tarihin marigayi Dan Maraya Jos | Amsoshin takardunku | DW | 29.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin marigayi Dan Maraya Jos

Dr. Adamu Dan Maraya dai ya bar duniya ba tare da samun haihuwa ba, to sai dai ya rike yara marayu da dama da suka girma a hanun sa, daya daga cikin su shi ne Alhaji Kuchili Dan Maraya.

Dan Maraya Jos Twitter Trauer im Netz

Marigayi Dr. Adamu Dan Maraya

Mai shekaru 69 da haihuwa a duniya, marigayin ya ziyarci kasashen duniya dabam- dabam sanadiyyar wakokinsa masu bada fuskanta game da zaman lafiya, hadin kan jama'a dama ilimantarwa kan sha'anin zamantakewar bil Adama.

Marigayi Dan maraya dai ya sami lambobin yabo da dama daga ciki da wajen Najeriya sabili da irin kwarewarsa wajen tsara wakokin da ke zamantowa tamkar karatu ga me saurare.

Dr. Adamu Dan Maraya dai ya bar duniya ba tare da samun arzikin haihuwa ba, to sai dai kuma ya rike yara marayu da dama da suka girma a hanun sa, daya daga cikin su shi ne Alhaji Kuchili Dan maraya.

Karte Nigeria mit den Bundesstaaten Adamawa, Bauchi und Plateau

Taswira da ke nuna garin Jos da Allah ya yo wa Dan Maraya rasuwa a cikinsa

Mai dakin Dr. Adamu Dan Maraya jos, Hajiya Hafsatu ta ce marigayin ya rike 'ya'yan da ke hanun sa marayu tamkar shi ya haife su.

Wasu abokan sana'ar Dr. Adamu Dan Maraya da suka hada da maroka, da mawaka, sun sheda cewar babu wata gaba ko kuma rashin jituwa da ake samu da shi a duk tsawon lokaci da suka yi suna tare da shi.

Alh, Mohammadu Baka rainuwa, wani fittacen sankira ne da suka yi zaman lafiya da marigayi har kusan shekru 60, ya tabbatar da hakan.

Hakan nan wasu da suka shedi halayen marigayi Dan Maraya Jos, mutane irin su Shehu Abdulkadir wanda akafi sani da ( Sardauna ) ya siffanta Dan Maraya matsayin matum mai kyauta da son jama'a har ma da dabbobi.

Dr. Dan Maraya Jos dai ya yi wakoki masu tarin yawa, to amma wakar da ke zamantowa karatu ga al'umma a koda yaushe, ita ce wannan wakar da ya yi mata lakabi Mutuwa Rigar kowa.