Tarihin Marigayi Amodu Shu′aibu | Amsoshin takardunku | DW | 20.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Marigayi Amodu Shu'aibu

Amodu Shu'aibu tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ya rigamu gidan gaskiyya a makon daya gabata 11.06.2016

Rayuwar marigayin, Amodu Shu'aibu na da ban al-ajabi, mutuwarsa tazo kusan kwanaki uku kacal a tsakaninsa, da mataimakinsa Stephen Keshi, wanda har shi, Amodu Shu'aibun yaje ta'aziyyarsa a gidan, ashe tasa na kusa,a inda ranar asabar bayan yayi sallar tarawiy da 'yan uwansa, a ranar Juma'a da aka je tashinsa sahur, sai aka tarar, rai yayi halinsa.

Shi dai, marigayi Coach Amodu Shu'aibu, an haife shi ne, a ranar 18 ga watan Afrilu, 1958, a garin da ake kira Okpella, cikin karamar hukumar Etsako, yabar buga kwallon kafa ne a sanadiyar karya kafa da yayi, yayin da yake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Niger Tonadoes FC, daga 1977 zuwa 1981, wanda daga bisani ya zamo mai horas da kungiyar kwallon kafa ta BCC Lions na Gboko, wanda har ya kaisu ga cin kofin kalubale ko kuma F.A Cup na Nigeria, har sau biyu ko uku, daga bisani ya ciyo kofin kalubale na CAF, wato kofin Afirka na kulob-kulob.

Fußballtrainer WM 2010 Shaibu Amodu Nigeria Flash-Galerie

Ya kuma rungumi kungiyar kwallon kafa na Elkenemi Warriors, wanda anan ma ya kaisu ga cin kofin kalubale na Nigeria, ya kuma horas da kungiyar IICC Shooting Stars, na Ibadan, da kuma Sharks na Port hacourt, kuma yaje ya horar da daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Afirka ta Kudu, wato Orlando Pirates.

Bayan ya dawo gida ne aka bashi alhakin horar da kungiyar kwallon kafa ta gida, wato Super Eagles, anan ma, ya kaisu ga shiga gasar kwallon kafa ta duniya, a shekara ta 2002, da 2010, ko da yake, duk a wadannan lokuta da ya kaisu, ba a barshi ya kaisu ga wasannin ba na ainihi, duk kuwa da cewa ya kungiyar Super Eagles din ga matsayi na uku, a gasar cin kofin kasashen Afirka da aka kara a kasar Angola, a shekara ta 2002, da kuma na uku, a makamancin wasan da aka buga a kasar Mali,a shekara ta 2010, abinda ake kallon rashin adalcin da mahunkar hukumar kwallon kafar Nigeria, suka yi masa.

Nigeria Fußball Nationalmannschaft Trainer Stephen Keshi

Marigayi Stephen Keshi wanda ya taba rike matsayin Super Eagles

Shi dai, marigayin ya rike mukamai da dama, da farko dai, ya rike mukamin mai horar da yan wasan 'Super Eagle' har sau uku, a 1998 zuwa da 1999, sai kuma a 2001 zuwa 2002, sai 2008 zuwa 2010. Sai daga bisani a 2013 aka sake dawowa dashi a matsayin 'Technical Director', wato mai kula, ko kuma mai tsara dabarun wasa na kungiyar kwallon kafar Nigeria, kuma yana kan wannan mukamin ne, Allah mai duka mai kowa, ya karbi ransa.

Har ila yau, marigayi Amodu Shu'aibu ya kasance mutum mai hakuri da juriya, a lokacin da ba a biyansu alawus-alawus dinsu,da albashinsu, amma za a kira shi, domin yayi aiki, kuma yakan bar duk abinda yake yi, domin rungumar aikin hannu biyu-biyu, domin kasarsa ce, ya bada gudumawarsa.

Ya dai, rasu ya bar mata (1) daya, da 'ya'ya (8) takwas, an kuma yi jana'izarsa a garinsu na Okpella, bisa tanadin addinin musulunci, kwana guda bayan rasuwarsa.