Tarihin Margaret Thatcher
April 15, 2013Iyayen Margaret Thatcher da farko talakawa ne, domin mahaifinta ta ya yi zaman saida kayan miya, kuma ita kanta da dinga kama masa aiki acikin shagon sayar da kayan miyar.kamin sannu a hankali ya shiga siyasa har ya kai ya zama magajin gari Grantham.
Lokacin da Thatcher ta shiga makaranta yarinya ce mai kwazo da niya wurin aiki.Tun daga Firamare har Sakadanre ta yi a makarantar garinsu, kamin daga baya ta shiga Jami'ar Oxford.Bayan haka ta yi aiki awata ma'aikata bincike da harhada magunguna.saidai banda haka kuma ta koma makaranta inda ta karanci shari'a daga shekara 1950 zuwa 1953
Shigar Margaret Thatcher cikin siyasa
Margaret Thatcher ta fara shawara siyasa tun tana 'yar makaranta,inda ta shiga jam'iyar da mahaifinta ke ciki wato jam'iyar Conservative.Ta fara shiga takara Majalisa a shekaru 24, wato a shekara 1950. to saidai a wannan karo ba ta yi nasara ba, domin mazabar da ta aje takara tamkar sansani ne na jam'iyar Labor.Bayan haka kuma ta sha shiga takara har dai hakarta ta cimma ruwa a zaben 'yan majalisa na shekara 1959.To tun daga wannan lokaci ba ta taba rasa zabe ba.
Banda Majalisa kuma ta sha rike mukamai ministan ilimi
Tafiya na tafiya har jam'iyar Conservative ta samu nasara a zaben shekara 1979 abinda ya ba Thatcher damar zaman Firaminista, kuma ta kasance ita ce macce ta farko a Turai da ta taba rike wannan mukami a lokacin.Ta rike wannan mukami tsawan shekaru 11 da rabi wanda shine wa'adin mulki mafi tsawa da wani Firaministan Birtaniya ya taba yi tun shekaru fiye da 200 da suka wuce.
Ta yi murabus daga karagar mulki ranar 28 ga watan Novemba na shekara 1990, bari mu saurari kadan daga jawabin da ta yi na saukarta daga aiki:
Ya ku 'yan uwa maza da mata wannan shine jawabi na karshe da zan yi ma ku a matasayina na shugabar Gwamnati.Bayan shekaru 11 da rabi na jagoranci, mu cimma nasarori da dama ta fannin aiyukan cigaban kasarmu, muna cike da farin cikin."
Bayann saukar Thatcher daga mulki ta i gaba da taka rawar siyasa.
Bayan Thatcher ta sauka daga mukamin Firaminista, wanda ya gajeta wato John Major ya nada a matsayin memba a Majalisar Dattawa ta kasa, har ma a shekara 1995 ya bada wata lambar girma wadda itace mafi daraja a Birtaniya.
Bayan saukar ta daga mulki Thatcher ta yi zagaye a kasashe da dama na duniya, inda ta dinga bada laccoci sannan kuma ta gudanar da aiyuka a karkashin Gidauniyar da ta girka.Daga shekara 2002,ta daina fitowa bainin jama'a akai-akai sabado rashin lafiya.Ta yi fama da cuttuta da dama wanda suka hada da hawan jiji da kuma cutar tsufa ta kibicewa har dai daga karshe ta kwanta dama ranar Takwas ga watan Afirilu na shekara 2013.
A lokacin da Margaret Thatcher ta shiga makaranta koyan aikin shari'a a shekara 1950 ,ta hadu da mutumen da ya zama mijinta wani mai suna Denis Thatcher.Sun yi aure ranar 13 ga watan Disemba na shekara 1951.Sun samu 'yan tagwaye biyu Mark da Carole.
Sannan kuma a siyasance ma ta bar magada masu yawa wanda za su cigaba da yada alkiblar tsarin mulkinta.
Baya ga wannan baiyani, a kasa za ku iya sauraran takaitacen tarihin Margaret Thatcher da wakilinmu na Landan Mohammad Sani Dauda ya aiko za ku iya sauraran.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman