Tarihin mai martaba Sarkin Mirriah Moutari Moussa | Amsoshin takardunku | DW | 22.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin mai martaba Sarkin Mirriah Moutari Moussa

Alhaji Moutari Moussa ya rike mukammai da dama na ayyukan hukuma tun lokacin Shugaban kasar Najar na farko, ya zuwa shekarar 2008 inda ya zama Sarkin Mirriah.

Shi dai mai martaba sarkin Mirriah mai ci yanzu Moutari Moussa, an haife shi ne a garin Mirriah a shekarar 1948 wanda bayan ya yi makarantar firamare a garin na Mirriah, kuma ya yi sakandire a garin Tasawa na jihar Maradi. Daga nan sai ya fice ya zuwa makarantar koyon ayyukan hukuma ta ENA da ke birnin Yamai, wanda bayan kammala wannan makaranta, ya dan taba aiki a ofishin ministan kudi. To bayan haka kuma a shekarar 1974 bayan da shugaba Seyni Kountche ya dauki mulkin kasar, an nada Moutari Moussa a matsayin shugaban gundumar Dakoro da ke cikin jihar Maradi, bayan nan, sai kuma aka nada shi mataimakin shugaban gundumar jihar Dosso wanda daga bisani kuma ya zamana shugaban gundumar ta Dosso baki daya.

Daga shugabancin gundumar Dosso na wancan lokaci sai kuma ya koma karo ilimi na shekaru uku, inda bayan fitowarsa, aka nada shi a matsayin shugaba gundumar Say da ke cikin jihar Tillabery. Bayan nan kuma sai ya koma a kasar Faransa ya karo ilimi, inda ya samu digri. Daga nan kuma sai aka nada shi a matsayin shugaban gundumar Tillabery. inda yana wannan matsayi, sai kuma shugaban kasa Seyni Kountche ya sake kiran shi, inda ya bashi nauyin jagorantar majalisar cigaban kasa wadda ake kira CND (Conseil National du Developpement) wadda ita ce ta shirya tsari na komawa ta farki na demokradiyya. Sannan kuma Moutari Moussa ya zama dan majalisar dokoki a karkashin Jamhuriya ta biyu lokacin mulkin Janar Ali Saibou, da kuma lokacin mulkin Shugaba Mahamane Ousmane, sai kuma a karkashin Jamhuriya ta hudu bayan da Shugaba marigayi Ibrahim Bare Mainasara ya hau mulki, Moutari Moussa ya zama shugaban majalisar dokoki. Sannan a Jamhuriya ta biyar ma dai ya sake zama dan majalaisa kuma shugaban gungun yan majalisu.

Bayan wannan lokaci kuma Moutari Moussa ya zama mai bai wa shugaban kasa Tanja Mamadou shawara na musamman. Bayan haka ne kuma sai Allah ya yi wa dan Uwansa mai martaba Sarkin Mirriah Souley Moussa Rasuwa, sai aka zabe shi a matsayin sabon sarkin Mirriah a shekarar ta 2008 inda ya zama shi ne sarki na 18 kawo yanzu.Kuma birnin Mirriah na a nisan km 20 a gabashin birnin Zinder bisa hanya mai zuwa Diffa.