Tarihin Kungiyar Tarayyar Turai | Amsoshin takardunku | DW | 18.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Kungiyar Tarayyar Turai

Kudirin kafa Kungiyar Tarayyar Turai ya samo asali jim kadan bayan Yakin Duniya na biyu, inda masu goyon bayan tsarin ke ganin haka ne kawai mafita daga kishin kasa.

A shekarar 1948 shekaru uku bayan kawo karshen Yankin Duniya na Biyu aka gudanar da taro a birnin Hague na kasar Netherland, wanda ke zama matakin farko na kafa wannan kungiya wadda a yau ta kunshi kasashe 28. Yarjejeniyar shekarar 1957 ake dauka a matsain wadda ta kafa kungiyar.

A wannan lokaci kasashe shida wadanda suka taka mahimmiyar rawa a yake-yake duniya: Belgium, da Faransa, da Italiya, da Luxemboug, da Netherland, da kuma Jamus ta Yamma sun kirkiro hanyoyin tuntubar juna da kuma chudanya.

Kasashen shida sun rantaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Rome na kasar Italiya a shekarar 1957, bisa kirkiro kasuwar bai daya, hade harkokin shige da fice na kayayyaki. Yarjejeniya ta fara aiki shekara guda bayan kulla ta a shekarar 1958.

A cikin shekarun 1960 kasashen Turai sun sake fuskantar zaman tankiya tsakaninsu. Amma duk da haka cikin shekarar 1965 kasashen sun sake amince da yarjejeniyar hadin kai, wanda aka saka mata hannu a birnin Brussels na kasar Belgium cikin shekarar 1967.

A shekarar 1973 aka fara fadada kungiyar ta Tarayyar Turai, wajen shigar da wasu kasashe. Tun daga wannan lokaci kasashen kamar Birtaniya, da Portugal, da Spain da kuma Girka sun samu shiga cikin kungiyar. Kuma domin shigar da kasashe Turai wadanda ke baya wajen karfin tattalin arziki da tsarin demokaradiya, cikin shekarar 1993 a birnin Copenhagen an tsara wani kundi wanda ya kunshi sharudan da kasashe za su cika kafin samun shiga cikin kungiyar. Kuma yanzu kasashe mambobin kungiyar 28 su ne:

Austriya, Belgium, Bulgariya, Birtaniya, Croatia, Cyprus, Jamhuriyar Czech, Denmark, Estoniya, Finland, Faransa, Jamus, Girka, Hungary, Ireland, Italiya, Latvia, Lithuania, Luxembourg, Malta, Netherland, Poland, Portugal, Romaniya, Slovakiya, Sloveniya, Spain, da Sweden.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar