Tarihin Konrad Adenauer | Amsoshin takardunku | DW | 10.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Konrad Adenauer

Konrad Adenauer ya jagoranci Jamus ta Yamma daga 1949 zuwa 1963.

ARCHIV - Alt-Bundeskanzler Konrad Adenauer auf einem Archivbild aus dem Jahr 1966. Der Todestag Konrad Adenauers liegt nun schon 42 Jahre zurueck, sein Amtsantritt gar 60 Jahre. Und doch ist der erste Kanzler der Bundesrepublik in den Koepfen der meisten Deutschen praesenter als viele seiner Nachfolger. Als Adenauer am 15. September 1949 Regierungschef wurde, konnte er auf eine reiche politische Erfahrung bauen. Schon 1917 war er Oberbuergermeister von Koeln geworden. 1926 wollten Parteifreunde ihn sogar zum Reichskanzler machen. (AP Photo) ** zu unserem Korr ** --- FILE - In this file picture taken in 1966, former German Chancellor Dr. Konrad Adenauer is shown. (AP Photo)

Konrad Adenauer

Konrad Hermann Joseph Adenauer wani fittacen ɗan siyasa ne da aka yi a nan Tarayya Jamus, wanda shine ma shugaban Jamus ta Yamma na farko bayan yaƙin duniya ya raba Jamus gida biyu.

An haife Konrad Adenauer a ranar Biyar ga watan Janairu na shekara 1876 wato shekaru 132 kenan baya a birnin Kolan.Ya fito daga wata babbar zuri'a ta kirista mabiya ɗarikar katolika.

Ya yi karatu ta fannin shari'a da kuma tattalin arziki inda har ya zama Dokta.

Tun ya na matashi Konrad Adenauer ya fara shawar harkokin siyasa.

Da farko ya shiga wata jam'iya mai matsakaicin ra'ayi da ke kira Zentrum Partei kamin daga bisani ya shiga jam'iyu CDU wadda a halin yanzu shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke jagoranta.

A cikinjam'iyar ta farko an zabe shi kansila har ma ya kai zama magajin garin birnin Kolan daga shekara 1917 zuwa 1933.

Dr Adenauer ya riƙe muƙamai da dama har ma amatakin gwamntain tsakiya tsakanin yaƙin duniya na farko da na biyu.

Misali ya yi zama memba kuma ya shugabanin hukumar ƙoli ta ƙasa daga 1920 zuwa 1933. To saidai ya fuskanci mummunar adawa daga jamusawa masu aƙidar Nazi saboda haka suka tuɓe shi daga duk wani muƙami a wannan shekara ta 1933, banda haka kuma suka tura shi kurkuku tare da zarginsa da kasancewa ɗan adawa ga 'yan Nazi.

A ƙarshen yaƙin duniya na biyu sai aka ci Jamus da yaki kuma ƙasashe da suka ci yaƙin suka yi watanda da ita.daga nan sai Amurikawa su ka sake ɗauko Konrad Adenauer suka damƙa masa jagorancin birnin Kolon kamin daga bisani turawan Ingila su tsige shi daga wannan matsayi.

French President Charles De Gaulle and his guest, West Germany's Chancellor Konhad Adenauer, stand upright in their car to review a parade of French and German troops at the Mourmelon training grounds near Reims, France, July 8, 1962. Adenauer currently is in France on an official visit. The two also visited nearby Reims Cathedral. (ddp images/AP Photo)

Konrad Adenauer da Charles de Gaulle

A wannan lokaci Dr.Konrad Adenauer na daga cikin jamusawan da ba su yanke ƙaunar sai ƙasarsu ta samu 'yancin ba, saboda haka su ka ƙirƙiro sabin jam'iyun siyasa, a wannan lokaci ne aka kafa jam'iyar CDU.Konrad Adenauer ya rungummi wannan jam'iya gaba gaɗe, inda har ma ya kai zama shine shugabanta a yankin Jamus da ke ƙarƙashin kulawar Ingila kamin daga baya a zaɓe shi shugaban CDU na ƙasa gaba ɗaya a shekara 1950.

Zaɓen Konrad Adenauer a matsayin shugaban gwamnatin Jamus ta Yamma.

Karo na farko an zaɓi Konrad Adenauer a matsayin shugaban gwamnatin Jamus ta Yamma ranar 15 ga watan Disemba na shekara 1949, sannan yayi tazarce a shekara 1953, sai kuma 1957 sai kuma zaɓen ƙarshe a shekara 1961.

Bari ma mu saurari kadan daga jawabin farko da Konrad Adenauer yayi gaban Majalisar Bundestag bayan zaɓen shi da akayi:Yaku maza da mata 'yan majalisa bayan dogon lokaci da mu ka share cikin yanayin ƙuncin, yanzu mun yi nasara girka Majalisa kuma mun zaɓi shugaban gwamnati.

Muna da jan aiki a gaban mu na sake gina wata sabuwar ƙasar Jamus.

Duk ya na shiga takara ne a ƙarƙashin tutar jam'iyarsa ta CDU tare da haɗin gwuiwa da CSU domin wannan jam'iyu biyu kamar Hasan da Husaini suke a nan Jamus, wato ako da yaushe su na tare.Wato idan aka yi lisafi ya yi kusan shekaru 15 Adenauer ya na jagorancin Jamus ta Yamma.

A lokacin mulkinsa Adenauer yayi gwagwarma ƙwarai da gaske ta fannin sake haɗewar Jamus wuri guda da kuma maidowa Jamus ƙimarta da martabarta ta hanyar ƙulla mu'amala da manyan ƙasashen duniya, wanda suka ci ta yaƙi kuma suka raba ta gida huɗu.

Dr. Konrad Adenauer (3.v.l.) und der sowjetische Ministerpräsident Nikolai Alexandrowitsch Bulganin (2.v.l.) beim Abschreiten der auf dem Moskauer Flughafen Pulkowo angetretenen Ehrenkompanie, aufgenommen bei der Verabschiedung des deutschen Bundeskanzlers aus Moskau am 14. September 1955. Adenauer hielt sich vom 8.-14. September 1955 mit einer Regierungsdelegation in Moskau auf und verhandelte über die Entlassung deutscher Kriegsgefangener aus der Sowjetunion.

Adenauer a Mosko 1955

A zamanin mulkinsa ne Jamus ta zama memba a ƙungiyar ƙasashen Turai a sherkara 1957, da kuma memba a cikin ƙungiyar tsaro ta NATO a shekara 1955.Sannan mutanen Bonn ba za su taɓa mantawa da shi ba domin shine ya tsaye sai birnin Bonn ya zama babban birnin Jamus ta Yamma.

Ranar 27 ga watan Maris na shekara 1952, Konrad Adenauer ya ƙetara rijiya da baya yayin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya shirya masa harin kwanta ɓauna sakamakon zargin da ake yi masa na shirin ƙulla hulɗa tsakanin Jamus da saɓuwar ƙasar Isra'ila.

A wani fanni kuma na diplomatiya Konrad Adenauer, ya ƙulla hulɗoɗi da Faransa a cikin wata yarjejeniyar da ya rattabawa hannu tare da shugaba De Gaule na ƙasar Faransa,yarjejeniyar da aka fi sani da yarjejeniyar Elysée wato fadar shugaban Faransa sun yi wannan yarjejeniya ranar 23 ga watan Janairu na shekara 1963.

ga ma kadan daga jawabin Adenauer a lokacin wannan mahimmin taro da ya hada Faransa da Jamus:Wannan sabuwar tafiya tsaknain Jamsu da Fartansa munyi imani zata zama ginshinƙin ma'amalar ƙasashen Turai.ƙasashenmu biyu za su yi aiki tuƙuru kafaɗa da kafaɗa, domin ganin hakan ta tabbata.

Sannan tare da Rasha ma sun cimma yarjeniyoyi da dama wanda su ka bada damar belin duban firsionin jamusawa a ƙasar Rasha wanda aka kama lokacin yaƙi duniya na biyu.

Wani abun tarihi kuma da Konrad Adenauer ya bari a Jamus shine girka rundanar soaj ta kasa domin bayan yaƙin duniya Jamus ta kasance ƙasa da ba ta da rundunar soja, to saboda haka bayan da Jamus ta yi nasara shiga memba a ƙungiyar tsaro ta NATO a 1955,sai ta samu damar girka rundunar tsaro ta ƙasa wato Bundeswehr.

Murabus ɗin Konrad Adenauer daga kujera mulki.

Bayan an zaɓi Adenauer a wa'adin mulki na huɗu, ya na tsakiyar wannan wa'adi sai ɓaraka ta fara samuwa a cikin jam'iyarsa ta CDU, aka yi ta ja in ja, a ƙarshe adi ya yada ƙwallon mungoro domin ya huta da ƙuda, wato yayi murabus daga muƙaminsa na shugabanin gwamnati.Yayi murabus ranar 15 ga watan Oktobar na shekara 1963.

Bayan haka, sai Majalisar Bundestag ta zaɓi ministan tattalin arziki wani mai suna Ludwig Erhard a matsayin wanda zai gaji Konrad Adenauer.

Adenauer ya rasu ranar 19 ga watan Afrilu na shekara 1967 a Rhöndorf wata unguwa dake birnin Bad Honnef a nan yankin Nord Rhein Westfaliya.

Bayan mutuwarsa saboda darajar da ɗaukaka da Konrad Adenauer ya samu akwai makarantu ,tinuna da dama wanda aka sama sunansa, domin tunawa da shi.Akwai ma wata gada a nan birnin Bonn mai suna Konrad Adenauer Brücke.

Manufofin Gidauniyar Konrad Adenauer

Wannan gidauniya da ake kira da jamusanci Konrad Adenauer Stiftung ko kuma kamar sauran irin gidauniyoyi ne na manyan jagororin duniya wanda suka yi suna su ke girkawa domin cigaba da taimakawa jama'a har ma bayan sun sauka daga muƙami.

A Amurika akwai musali Bill Clinton Fondation kokuma Faransa Fondation Jaques Chirac kokuma akwai masu kuɗi suma da ke girka irin wannan gidauniya kamar misalin Gidauniyar Bill gates shaharraren mai kunɗin na na Amurika, ko kuma Gidauniyar Moo Ibrahim shima shaharraren mai kuɗi na ƙasar Sudan.

To idan mu ka dawo kan Gidauniyar Konrad Adenauer , da farko ta na da alaka ne da wata kungiya ta addini hasali ma wada ke gwagwarmayar yada tarbiya mai nasaba da darrikar romankatolika da kuma tarbiyar siyasa rinta demokradiyya.Da jamusanci,wannan ƙungiya ana ce mata Gesellschaft für Chirstilch-demokratische Bildungsarbeit,a n girka ta a shekara 1956, kuma tun daga shekara 1964 aka rada mata sunan Konrad Adenauer.

A yanzu haka wannan gidauniya ta na tafiya bisa aƙidojin Adenauer wata ilmantarawa, girka demokarɗiya, sannan ta kan biya kuɗaɗen karatu ga mutanen dajke da hazaƙa amma ba su da damar su biya wa kansu kudin karantu su cigaba da ilmi mai zurfi.

Titel: GMF Logo Konrad Adenauer Stiftung Format: Artikelbild Bildrechte: Verwertungsrechte im Kontext des Global Media Forums eingeräumt.

Wannan gidauniya ta na aiki matuƙa ta fannin ƙara samun haɗin kan ƙasashen Turai da kuma cudaya tsakanin ƙasashen duniya.

Gidauniyar Konrad Adenauer na aiki ƙwarai a ƙasashen na Afrika ta fannin wayar da kai dangane da tsarin mulkin demokraɗiya,kare haƙoƙin bani Adama, da samar da ilimi.

An ce ko wace shekara Gidauniyar ta na kashe tsabar kuɗi Euro miliyan ɗari.Duk da cewa dai tambayar ba ta shafi Gidauniyar Konrad Adenauer ba amma ya na da kyau mu gutsuro mamsu saurao kadan daga aiyukan wannan Gidauniya, sannan kuma mu yi fata shugabanin Afrika za su koyi da irin su Konrad Adenauer ,domin idan su ka yi haka, babu shakka ƙasashenmu za su daina tara hannu kullum wajen neman taimako.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammed Abubakar