1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Jose Mourinho

June 21, 2013

Jose Mourinho guda ne daga cikin masu horas da 'yan wasa da ya yi suna saboda nasarorin da ya samu daga fara wannan sana'a kawo yanzu.

https://p.dw.com/p/18uGm
Real Madrid's coach Jose Mourinho waits for the start of their Spanish King's Cup quarter-final second leg "El Clasico" soccer match against Barcelona at Nou Camp stadium in Barcelona January 25, 2012. REUTERS/Albert Gea (SPAIN - Tags: SPORT SOCCER HEADSHOT)
Jose MourinhoHoto: REUTERS

An haifi José Mário dos Santos Mourinho wanda aka fi sani da suna Jose Mourinho a ranar ashirin da shidda ga watan Janairu shekara ta 1963 kasar Portugal kuma kamar kowanne mutum ya yi karatunsa na boko a kasar ta su.

Mourinho wanda ake wa lakabi a fagen wasan kwallon kafa da 'Special One' ya fara yi aiki a masatyin malamin makaranta da ke koyar da abubuwan da su ka danganci motsa jiki. Daga bisani kuma sai ya shiga harkokin wasan kwallon kafa a matsayin dan wasa sannan ya fara horas da wata kungiya ta matasa a kasarsa ta haihuwa.

Jose Mourinho ya yi aiki da Sir Bobby Robson a mastayin tafintansa lokacin da ya ke kungiyar kwallon kafa ta Sportin Lisbon da kuma Porto a kasar Portugal gami da Bercelona a kasar Spain. Bayan da Robson ya raba gari da wadannan kulabluka, Mourinho ya cigaba da kasancewa tafinta inda ya yi aiki da magajin Robson wato Louis Van Gaal.

Bayan da Jose Mourinho ya dau tsawon lokaci ya aiki a mastayin tafinta, daga baya sai ya shiga harkar horas da 'yan wasa gadan-gadan inda ya fara da kasancewa mataimakin kocin Benfica a shekara ta 2002.

Haka dai ya cigaba da aikinsa har sai a shekara ta 2004 inda ya sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea wanda zuwansa ya sanya kulab din lashe gasar Firimiya ta Ingila da kuma kofin Champions League.

A iya lokacin da ya share a masatyinsa na kocin Chealse daga shekara za 2004 zuwa 2007, kulab din ya samu cigaba matuka gaya wanda ya sanya ya zama gagara badau kuma wannan nasara da kulab din ya samu karkashin jagorancin Mourinho ya sanya 'the special one' kamar yadda ake masa lakabi yin suna matuka.

Lokacin da ya bar Chealsea, Mourinho ya koma Italiya inda ya kasance da Internazionale na tsawon shekaru uku inda ya samu nasarar kaiwa ga lashe gasar Serie da kuma kofin champions league, sai kuma daga bisani ya koma kulab din Real Madri a shekara ta 2010 zuwa farkon wannan shekarar inda ya koma kulab din Chelsea a matsyin mai horas da 'yan wasan.

Tarihi dai ba zai mance da Mourinho ba saboda kokarin da ya yi na lashe kofin champios league da kulabluka biyu baya ga sauran nasarori da ya samu a wuraren da ya yi aiki wanda ya sanya ma'abota wasan kwallon kafa ke kallonsa da matukar kima a fage tamaula.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar