Tarihin gasar wasannin Commonwealth | Amsoshin takardunku | DW | 18.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin gasar wasannin Commonwealth

Gasar wasannin Commonwealth dai ta samo asali ne tun a shekarar 1891 wato shekaru 123 da suka gabata ke nan.

Wani limamin Kirista Rev. John Astley Cooper ne dai ya rubuta sharhi a jaridar Times ta Ingila, inda ya yi kiran shirya wasannin sada zumunci a tsakanin kasashen da ke karkashin mulkin mallakar Ingila a wannan lokacin. To amma sai a shekarar 1930 ne aka yi wasanni na farko a birnin Hamilton na kasar Canada. A shekarar 1934 kuma aka yi wasanni na biyu a Ingila. A lokacin wasannin farko a birnin Hamilton kasashe 11 ne suka tura 'yan wasa 400 domin shiga wasanni guda shida da za a fidda gwani a gasa 59. Tun daga lokacin ne ake shirya wasannin duk bayan shekaru hudu, wanda kuma tun da aka fara sai a shekarun 1942 zuwa 1946 ne kadai ba ayi wasannin na Commonwealth ba sabo da yakin duniya na biyu. Bayan nan ne kuma aka yiwa tsarin wasannin garambawul musamman a shekarar 1954 inda aka canzawa wasannin suna da wasannin daular Birtaniya da kasashen Commonwealth kuma a shekara ta 1974 aka sake sauyawa wasannin suna da wasannin kasashen da suka taba zama karkashin mulkin mallakar Ingila. A wasannin shekara 1978 ne a Edmonton na kasar Kanada aka radawa wasannin sunan da akekiransa da shi a yanzu wato wasannin Commonwealth.

A yanzu dai akwai kasashe 53 da suka taba zama karkasin renon Ingila a kungiyar ta Commonwealth in ka cire kasar Gambiya da ke Afirka ta Yamma wadda ta janye kanta daga kungiyar bisa nuna fushi kan zargi da kuma Allah wadai da gwamnatin Birtaniya ta yi wa shugabannin kasar ta Gambiya kan take hakkin dan Adam. Akwai kuma kasashe 18 wadanda duk da suna da 'yancin kansu to amma suna karkashin shugabancin sarauniyar Ingila ne. Sa'annan sai kasashen da ke cikin hadaddiyar daular da suka hada da Ingila da Wales da Scotland da kuma Ireland ta Arewa. A nahiyar Afirka in ka cire Gambiya kasashe 18 ne suka shiga wasannin a bana da aka gudanar a birnin Glasgow kasashe 12 kuma daga nahiyar Amirka da tsibiran Oshiyaniya da kuma wasu kasashe 11 da har yanzu suke karkashin mulkin mallakar Birtaniya.

Sai dai kuma duk da yawan kasashen Afirka da ke halartar wasannin na Commonwealth, babu wani birni a nahiyar da ya taba daukar bakuncin wasannin. Ga misali idan aka gudanar da wasanni na shekarar 2018 a birnin Gold Coast na jihar Queensland da ke kasar Australia, kasar za ta dauki bakuncin wasannin kenan har karo biyar. Bugu da kari kuma Birtaniya ta dauki bakuncin wasanni sau 18 daga cikin wasannin. Baki daya daga cikin wasanni 53 da aka yi 46 daga ciki an gudanar da sune a tsakanin kasashen Birtaniya da Australia da Canada da kuma Newzealand. A shekara ta 2010 kasar Indiya ta dauki bakuncin gudanar da gasar wasannin na kungiyar Commonwealth karo na 19 inda aka gudanar da shi a birnin New Delhi. Bayan kammala wasannin bana da aka gudanar a birnin Glasgow Shugaban kwamitin gudanar da harkokin wasanni a kasar Afirka ta Kudu Gedeon Sam ya sanar da cewa birnin Durban zai shiga takarar daukar bakuncin wasannin a shekara ta 2022.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal