Dan Dicko Dan Koulodo yana koyarwa kuma yana bin bincikensa lokacin da mutuwa ta riskeshi. Dan Dicko Dan Koulodo ya sami takardar shaidar kimiyyar hada sinadarai a jami'ar Bordeaux a 1954.
An haifi Dan Dicko Dan Koulodo a 1934 a Maradi.Tsakanin 1955 zuwa 1957, ya sami digiri a kimiyyar hada sinadarai a jamiar Montpellier. Ya karanci kimiya da fasaha daga 1958 zuwa 1959 kafin ya yi digiri na uku a Marseille a Faransa a 1967. Daga kasa za ku iya sauraran sauti na tarihinsa.