Tarihin Dioncounda Traore shugaban riƙwan ƙwarya na ƙasar Mali | Amsoshin takardunku | DW | 10.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Dioncounda Traore shugaban riƙwan ƙwarya na ƙasar Mali

An haifi Dioncounda Traoré ranar 23 ga watan Faburairu na shekara 1942 a garin Kati na ƙasar Mali.

GettyImages 158217193 Mali's interim government President Dioncounda Traore makes a statement in Bamako on December 11, 2012 accepting Prime Minister Cheick Modibo Diarra's resignation, and said he will appoint his successor 'within 24 hours'. Prime Minister Cheick Modibo Diarra resigned on December 11 just hours after former coup leader Captain Amadou Sanogo ordered soldiers to arrest him at his home, plunging Mali deeper into chaos after Islamist rebels seized the north. AFP PHOTO / HABIB KOUYATE (Photo credit should read HABIB KOUYATE/AFP/Getty Images)

Dioncounda Traore

Dioncounda Traoré an haife shi ranar 23 ga watan Faburairu na shekara 1942 a garin Kati na ƙasar Mali, yanzu ya na da shekaru 71 a duniya.A nan garin Kati ya shiga makarantar firamare, sannan ya cigaba a garin Nara.

A shekara 1961 ya samu takardar shaidar shiga jami'a a wata makaranta mai suna Terrasson de Fougéres dake Bamako, babban birnin ƙasar Mali.Ya cigaba da karatu a jami'o'in ƙasashe daban-daban kamar Rasha, Aljeriya da kuma Faransa.Ya yi karatu ta fannin ilimin lissafi ko kuma mathematics inda har ya samu digirin digir-digir a wannan fanni.

Mali's interim President Dioncounda Traore (C) arrives at the main airport in the capital Bamako, July 27, 2012. Mali's interim president returned on Friday from weeks convalescing abroad after he was beaten up by a mob, facing pressure to form a new government and authorise a foreign military intervention against rebels in the north. Mali needs outside support to recover from twin crises sparked by a March coup in the capital that precipitated the rebel takeover of its northern zones, occupied by Islamists dominated by al Qaeda's North African wing, AQIM. Picture taken July 27, 2012. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: POLITICS CIVIL UNREST CONFLICT)

Dioncounda Traore da tsofan Firimiya Cheik Modibo Diara

Bayan ya kamalla karatu yayi koyarwa jami'o'i da kuma makarantu a ƙasar Aljeriya.

Sannan yayi zaman koyarwa a makarantar koyan husa'o'in shugabanci da ke birnin Bamako.A nan ne hukumomin wancen lokaci su ka cafke shi tare da zargin sa da hannu cikin gwagwarmayar ƙwatar 'yancin ma'aikata,saboda haka a ka yi awan gaba da shi zuwa yankin arewacin Mali, kamin daga bisani a tsige shi kwata-kwata daga aikin gwamnati.Hakan ta faru a shekara 1980.Ya yi zama ba aiki har tsawan shekaru biyu kamin daga baya a maida shi.To amma hausawa ke cewa wai hali zanen duste duk da wahalhalun da ya sha ba ta naha shi lokacin da aka maida shi aikin ya ci gaba kuma da kokowar neman 'yancin ma'aikata, saboda haka kuma a sake tsige shi daga aikin gwamnati a shekara 1986.

Ya sake dawowa aiki a shekara 1991 bayan da sojoji suka kifar da mulkin shugaba Moussa Traoré.Tun daga wannan lokaci ya riƙe muƙamai daban-daban a harkokin

Yaushe Traore ya shiga harkokin siyasa har ta kai shi ga zama shugaban ƙasa na riƙwan ƙwarya?

Dionconda Traoré tun ya na matashi yake shawar siyasa.

A lokacin da ya na ɗan makaranta ya riƙe mukamai daban-daban a cikin ƙungiyoyin 'yan makaranta.Bayan da ya kamalla karatu ya fara riƙe mukaman siyasa a shekara 1992, inda aka naɗa shi ministan ƙwadago, sannan ya riƙe ministan tsaro daga 1993 zuwa 1994 , sannan ya riƙe muƙamin ministan harkokin wajen ƙasar Mali,tsawan shekaru uku daga 1994 zuwa da 97.

Links: Coup leader Captain Amadou Sanogo attends a ceremony as former parliament speaker Dioncounda Traore (unseen) is sworn in as Mali's interim president in the captial Bamako, April 12, 2012. Traore took over as Mali's interim president on Thursday from the leaders of last month's coup, promising to hold elections and fight Tuareg and Islamist rebels occupying half the country. Traore, 70, a labour activist turned politician, was sworn in by Supreme Court President Nouhoum Tapily in the capital Bamako as part of a deal to restore civilian rule after army officers staged a March 22 coup in the West African state. REUTERS/Malin Palm (MALI - Tags: POLITICS MILITARY PROFILE) Rechts: Mali's interim President Dioncounda Traore speaks during a news conference at the presidential palace in Abidjan May 16, 2012. REUTERS/Luc Gnago (IVORY COAST - Tags: POLITICS HEADSHOT)

Dioncounda Traore da Amadou Hayya Sanogo

Lokacin da guguwar siyasa ta kaɗa a ƙasar Mali ya shiga wata jam'iya mai suna Adema PASJ inda aka zaɓe shi mataimakin shugaba na biyu, sannan mataimakin shugaba na farko.Lokacin da aka shirya zaɓe a shekara 1997 an zaɓe shi dan majalisar dokokin ƙarƙashin wannan jam'iya a mazaɓar Nara.A cikin Majalisar, sauran abokansa suka naɗa shi a matsayin shugaban rukunin 'yan majalisar Adema PASJ.

A shekara 2000 lokacin da tsofan Firaministan Mali Ibrahim Bubakar Keita ya fita daga jam'iyar Adema sai aka zaɓi Dioncounda Traoré a matsayin shugaban wannan jam'iya.

An sake shirya zaɓe a ƙasar Mali a shekara 2002, kuma aka sake zaɓen shi ɗan majalisa, ya kuma ƙara yin tazarce a shekara 2007.

A wannan shekara jam'iyar Adema PASJ ta taka mahimmiyar rawa a zaɓen, dalili da haka 'yan majalisa masu rinjaye su ka zaɓi Pr Dioncounda Traoré, a matsayin kakakin Majalisar Dokokin ƙasar Mali.Ya na riƙe da wannan matsayi ne sojoji suka kifar da shugaban ƙasa Amadou Toumani Touré a watan Maris na shekara 2012.Kamar yadda aka sani, Mali na cikin shirin zaɓen shugaban ƙasa juyin mulkin ya faru, kuma har jam'iyar Adema PASJ ta tsaida Dioncounda Traoré a matsayin ɗan takararta a wannan zaɓe.

Bayan juyin mulkin sai ya tafi gudun hijira a Burkina Faso.

To saidai dalili da mummunar adawa da ƙungiyar ECOWAS da gamayyar ƙasa da ƙasa suka nuna ga wannan juyin mulki cilas kaptan Amadou Hayya sanogo da ya jagoracin sojoji, ya sauka daga karagar mulki, kuma kamar yadda kudin tsarin mulkin Mali yayi tanadi, idan babu shugaban ƙasa kakakin Majalisa ke hawa mulkin riƙwan ƙwarya.

France's President Francois Hollande (L) is welcomed by Mali's interim president Dioncounda Traore upon his arrival at Sevare, near Mopti, on February 2, 2013. President Francois Hollande visits Mali as French-led troops work to secure the last Islamist stronghold in the north after a lightning offensive against the extremists. Hollande will head to Timbucktu and Bamako. AFP PHOTO / PASCAL GUYOT (Photo credit should read PASCAL GUYOT/AFP/Getty Images)

Dioncounda Traoré da François Hollande

Bisa shiga tsakanin ECOWAS shugaban da aka hamɓare wato ATT, ya ce ya rungummi ƙaddara, ya amince ya sauka daga mulki,saboda haka aka hauda Dioncounda Traoré a matsayin shugaban ƙasa na riƙwan ƙwarya.Ya dawo daga gudun hijira a Burkina Faso ranar bakwai ga watan Afrilu na shekara 2012, an rantsar da shi ranar 12 ga watan na Afrilu.

Saidai wani abinda da tarihin zai riƙe daga cikin rayuwar Pr Dioncounda Traoré shine dukar tsiya da wasu mutane su ka yi masa wanda ake zargin cewar masu goyan bayan sojojin da suka yi juyin mulki ne, a fadarsa ta shugaban ƙasa ranar 21 ga watan Mayu na shekara 2012.Sun ji masa rauni mai tsanani saboda haka cilas ya tafi jiya ƙasar Faransa, har tsawan watani biyu.

Sannan wani ƙarin baiyani da tarihi zai riƙe game da Traoré shine kiran da yayi wa shugaban Faransa François Hollande domin ya taimako masa da sojoji domin ƙwato yankin arewacin ƙasar dake cikin hannun ƙungiyoyi masu tsatsauran kishin addinin Islama.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu