Tarihin Alhaji Abubakar Imam | Amsoshin takardunku | DW | 01.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Alhaji Abubakar Imam

An haifi Abubakar Imam a garin Kagara na jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya a shekara ta 1911. Marigayin ya yi fice wajen rubutun kagaggun labarai na Hausa.

Bücherregal

Abubakar Imam ya taimaka wajen habaka adabin Hausa saboda irin rubuce-rubucen da ya yi.

Abubakar Imam ya yi karatunsa na boko a jihar Katsina a makarantar nan ta Middle School da ke Katsina da kuma Katsina Training College sannan ya yi karatu a tsangayar ilimi ta jami'ar London da ke Burtaniya.

Bayan da ya kammala karatunsa, ya yi koyarwa a Katsina sannan kuma ya yi aiki matsayin edita na jaridar nan ta Gaskiya Ta Fi Kwabo kana ya tallafawa masarautar Katsina ta wancan lokacin karkashin shugabancin Alhaji Muhammadu Dikko inda ya ke fassara rubuce-rubuce daga Larabaci zuwa harshe Hausa.

Alhaji Abubakar Imam ya yi fice ne lokacin da aka sanya wata gasa ta rubutun kagaggun labarai a shekara ta 1933 inda wani littafi da ya rubuta mai suna Ruwan Bagaja ya yi nasara a cikin litattafan da aka rubuta. To baya ga wannan littafi, marigayin ya kuma rubuta wasu litattafan da dama da suka hada da Magana Jari da Ikon Allah da Tarihin Annabi (S.A:W:S) da Tarihin Musulunci da Auren Zobe da makamantansu.

Marigayi Abubakar Imam na daga cikin marubutan da dalibai a matakai daban-daban ke yin nazari kan littafan da suka rubuta da ma nazari kan rayuwarsu. Allah ya yi masa rasuwa cikin shekara ta 1981 ya kuma bar yara goma sha hudu, maza bakwai da kuma mata bakwai.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal