Tarihin Ahmet Kenan Evren | Amsoshin takardunku | DW | 18.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Ahmet Kenan Evren

An haifi Ahmet Evren tsohon shugaban ƙasar Turkiyya a a ranar 17 ga watan Juli na shekara ta 1917 a garin Alasehir.

Kenan Evren ya shiga aikin Soja a shekara ta 1938 wato shekarar mutuwar Mustafa Kemal Ataturk wanda ya kafa jamhuriyar ƙasar Turkiyya ta zamani.Ya zamo shugaban habsan sojojin ƙasar ta Turkiyya a shekara ta 1978.A shekara ta 1980 ya jagoranci wani juyin milki da sojoji su ka yi wa gwamnatin firaminista Suleiman Demirel tare da canza kundin tsarin mulkin ƙasar domin maye shi da wani sabo da ke bai wa mulkinsa cikakken iko tare da rusa majalisar dokoki dama haramta duk wasu jam'iyyun siyasa.

Domin jin ƙarin bayani sai a saurari shirin

Sauti da bidiyo akan labarin