Tarihin ƙungiyar ′yan tawaye na M23 na Kwango | Amsoshin takardunku | DW | 30.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin ƙungiyar 'yan tawaye na M23 na Kwango

An kafa ƙungiyar wacce galibi ta ƙunshi tsofin dakarun gwamnati yan ƙabilar tutsi a shekara ta 2009 ,saboda rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma

A cikin yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin Joshephe Kabila mai matakai ɗaya ɗaya har guda 15 ta tanadi cewar tsofin bradan yan tawayen za a saka su cikin rundunar sojojin gwamnatin Kwango ta FARDC a lokacin ne gwamnatin ta ɗauki janar Bosco Ntaganda da kanal Sultani Makenga ta saka su a cikin rundunar sojojin tare da wasu tsofin yan tawayen.

Kama Laurent Nkounda ya ƙara asasa tawayen a Kwango

Titel: Rebellenführer Makenga Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Simone Schlindwein Wann wurde das Bild gemacht?:30.11.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Goma, Ostkongo Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Rebellenchef Sultani Makenga

Kanal Sultani Makenga

Makonnin kadan bayan haka ne a ka kame tsofohon jagoran yan tawayen Laurent Nkounda a Ruwanda kuma wanda kanal sultani yake ji so sai kuma za a iya cewar na hannun damar sa ne.To tun a lokacin ne kanal makenga wanda ke cikin dakarun gwamnatin kana tsohon dan tawayen na CNDP ya ba da sanarwa cewar sun farfaɗo da ƙungiyar ta yan tawayen ta CNDP wacce suka ba ta yanzu sunan M23 wanda ke da asili akan yarjejeniyar da aka cimma a ranar 23 ga wata Maris wannan shine mafarin M23.Sannan a lokacin ne Makenga da wasu sojojin suka ficce da ga cikin rundunar sojojin Kwango ya ce kuma sun kori janar Bosco Ntaganda ɗaya daga daga cikin ya'yan ƙungiyar domin sun zarge shi da cewar da shi gwamnatin ta haɗa baki ta kama janar Laurent Nkounda a cikin watan Mayo na shekara ta 2009.Kuma lokaci ne gwamnati Kabila ta yi amfani da wannan ɓaraka ta yan tawayen ta ba da waranti Bosco wanda daman ya zame mata ɗan gadangaran bakin tulu;wanda kotun duniya ke naman sa ruwa jallo akan laifukan yaƙi kusan shekaru shida da suka wucce.

Da ga bisani 'yan tawayen sun sauya buƙatu

M23 rebels withdraw from the Masisi and Sake areas in the eastern Congo town of Sake, some 27 kms west of Goma, Friday Nov. 30, 2012. Rebels in Congo believed to be backed by Rwanda postponed their departure Friday from the key eastern city of Goma by 48 hours for “logistical reasons,” defying for a second time an ultimatum set by neighboring African countries and backed by Western diplomats. The delay raises the possibility that the M23 rebels don’t intend to leave the city they seized last week, giving credence to a United Nations Group of Experts report which argues that neighboring Rwanda is using the rebels as a proxy to annex territory in mineral-rich eastern Congo.(Foto:Jerome Delay/AP/dapd).

Dakarun ƙungiyar ta M23

Tun daga wannan lokaci ne kuma yan tawayen na M23 suka ɗauki makamai suka koma daji suna yaƙar gwamnati Kabila kan cewar ya mutunta yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2009 ta rana 23 ga watan Maris. To amma daga bisannin kungiyar yan tawayen ta kawo wasu buƙatu na siyasa baya ga buƙatar da ta gabatar ta saka bradanta cikin rundunar sojojin ƙasar kanan a bar su, su yi aiki a yankin su na gabashi domin kare al'ummar su wato a yanki arewa maso gabashin Kivu.

Yunƙurin shiga tsakani na ƙungiyar ƙasashen yankin Grand Lac

(L-R) Kenya's President Mwai Kibaki, President of the Democratic Republic of Congo Joseph Kabila and Uganda's President Yoweri Museveni pose in Kampala on November 24, 2012 as they attend an extraordinary summit of the 11-member regional bloc, the International Conference on the Great Lakes Region (ICGLR). Regional leaders called on DR Congo rebel group M23 today to end hostilities and relinquish a key eastern town it seized in an advance that has sparked fears of a wider conflict. AFP PHOTO/ PETER BUSOMOKE (Photo credit should read PETER BUSOMOKE/AFP/Getty Images)

Taron ƙasashen yankin Grand Lac a Kampala

Buƙatun na siyasa su ne a daina yiwa jagoran yan adawar ɗaurin talala sannan a rusa hukumar zaɓe.ƙungiyar dai ta na dakaru sama da 1500 kuma suna da sansani a yankin gabashi na ƙasar kan iyaka da Ruwanda wacce ake cewar ta na tallafa masu.Yunƙurin su na baya baya nan shi ne na kame garin Goma a ranar 16 ga watan Nuwamba na shekara ta 2012 da ya gabata bayan an dakatar da buɗe wuta a tsawon watanni ukku a yaƙin da sama da mutane 113 suka mutu kana ya tilasawa wasu mutane dubu 230 suka ƙauracewa yankin arewacin Kivu kafin daga bisannin ƙuniyar ƙasaShen yankin Grand Lac ta shiga tsakani su janye daga Goma.Wani abin la'akari a nan shi ne cewar tun lokacin da ƙungiyar ta 23 ta sake koma wa yaƙi a gabashin Kiwu ake ta samu yawaitar ƙananan ƙungiyoyin yan tawAyen har kusan guda 30, kuma ta ƙarshe ita ce mai sunan URDC mai fafutukar tabbatar da tsarin dimokaradiyya a Kwango.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu