Tarihi da manufar ′yan Anti-Balaka na Bangui | Siyasa | DW | 10.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tarihi da manufar 'yan Anti-Balaka na Bangui

Dakarun sa kai na Anti-Balaka na cin karensu ba tare da babbaka ba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda baya ga kashe musulmi suke kuma kokkonasu tare da cin namansu. To wai shi su wa 'yan anti-Balaka?

Borab dai, daya ne daga cikin unguwanni Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda matasan da ke dauke da adduna da kuma bindigogi ke shafe yini suna yin sintiri. Ana dai danganta Borab da matattarar 'yan bindigan sa kai na Anti-Balaka. A wannan unguwa ne ma dai cibiyarsu ta ke. Sannan kuma a nan ne gidan Francois Bozize da 'yan tawayen Seleka suka hambarar daga kujerar mulki a shekarar da ta gabata ya ke.

A Borab din ne ma dogaransa da dama da kuma wasu abokan burmin siyasan tsohon shugaban ke ci-gaba da fakewa. Hasali ma dai a wannan unguwa ce matasan da ke goyon bayan Bozize suka fara hada karfi da karfe domin kare kansu daga ta'asar da 'yan Seleka suka aikata a inda baya ga kwasar ganima suka kuma fyade mata da dama.

Dalilan kafa Anti-Balaka a Bangui

Zentralafrika Milizkämpfer Soldat 23.01.2014

Sojojin Faransa ba su yi nasarar ja wa 'yan Anti-Balaka birki ba

Su dai 'yan Anti-Balaka suna rataya jerin layu da sauran kayan tsatsube a wuyarsu, yayin da suke daura guru a katararsu, domin kare kansu daga harbin bindiga na abokan gaba 'yan Seleke. Ko da shi ma Gomez, wani kakakin 'yan Anti-Balaka, sai da ya ce raba sunansu da irin wannan kayan tsatsube tamkar dai tuya ce a manta da albasa.

"Sunanmu ya samo asali ne daga kariyar da muke neman daga harsashin bindiga AK 47. Kungiyar ma na da dogon tahiri. An kafa Anti-Balaka ne domin yakar 'yan fashi da makami da suka addabi al'umma tare da kamesu, tun ma kafin Bozize ya hau kan kujerar mulki. Amma sakamakon musguna wa al'umma da 'yan Seleka suka yi bayan da Djotidia ya hau mulki ne, muka yanke shawarar sake farfado da kungiyar domin yakar wadannan 'yan tawayen."

Akasarin mayakan sa kai na Anti-Balaka dai matasa ne da ba su yi karatu da rubutu ba. Wadansunsu ma da na da kasa da shekaru goma da haihuwa. Lamarin da ke sa su neman daukar fansa a kan abokan gaba, sakamakon kisar gilla da aka yi wa iyayensu; kamar yadda daya daga cikinsu ya bayyana.

"Ni kadai na saura a cikin dangina. Lokacin da 'yan Seleka suka mayar da Bangui karkashin ikonsu ne suka harbe mahaifina. Watanni biyu bayan haka kuma suka sake dawowa, saboda suna ganin cewa mahaifina ya boye makamai a cikin gidanmu. Mahaifiyata da 'yar uwata sun yi musu bayanin cewa babu makamai. Amma kuma 'yan Seleka ba su yarda ba. Saboda haka ne suka harbesu. Sa'ar da na ci shi ne bana kusa. Saboda haka ne na tsira da raina. Lokacin da na dawo kuma ba abin da na samu sai gawarwakinsu."

Yadda Anti-Balaka ta canja manufofinta

Sebastien Wenezoui Zentralafrikanische Republik 16.01.2014

Na hannun daman Francois Bozize sun kakkange Anti-Balaka

Dubban matasa maza da mata da suka rasa iyayensu ne suka kasance a rukunin farko na mambobin Anti-Balaka. Ana dai basu adduna da kuma wukake da ma dai miyagun kwayoyi a wasu lokutan domin su shiga a fafata dasu. Dukkaninsu sun yi imanin cewa wadannan layu da sauran kayan tsatsube da suke amfani da su za su karesu daga bindiga da 'yan Seleka ke harba musu. Sai dai kuma neman rama wa kura aniyarta da suke yi na kai 'yan anti-balaka daddatsa musulmi gunduwa-gunduwa tare da cin namansu.

Da farko dai 'yan anti-Balaka sun ce suna gaggwarmaya ne domin kare garuruwansu da unguwanninsu daga cin zali. Sai dai kuma sannu a hankali tsofoffin sojojin kasar da kuma magoya bayan tsohon shugaban Bozize suka fara kakkange harkokin wannan kungiya. Hasali ma dai tsohon ministan da ke kula da harkokin matasa a gwamnatin Francois Bozize kana shugaban hukumar kwallon kafar wannan kasa, Patrice Ngassona ne shugaba 'yan Anti-Balaka.

Mawalafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba

Sauti da bidiyo akan labarin