Tarayyar Turai za ta ci gaba da taimakon Cyprus | Labarai | DW | 20.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai za ta ci gaba da taimakon Cyprus

Majalisar Dokokin Cyprus ta yi fatali da shirin tatsan kudaden masu ajiya a Bankuna.

Ministocin kudi na kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro, sun ce a shirye su ke wajen taimakon kasar Cyprus, bayan majalisar dokokin kasar ta yi watsi da shirin karbar kudaden haraji daga masu ajiya a bankuna.

Kasashen na Turai sun bukaci gwamnatin kasar ta kirkiro hanyar samun kimanin Euro miliyan dubu biyar, a matsayin sharadin da zai kai kasar ta samu kudaden ceto tattalin arziki, wanda haka zai kare tattalin arzikin kasar daga rushewa.

Tuni kafofin yada labaran kasar su ka fara nunar da cewa gwamnati ta fara tunanin wasu hanyoyin samun kudaden. Kazalika, babban bankin Turai ya ce zai ci gaba da daukan matakan bayar da tallafin tattalin arziki ga kasar ta Cyprus.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh