Tarayyar Turai ta ninka kudade ga G5 Sahel | Labarai | DW | 23.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai ta ninka kudade ga G5 Sahel

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin ninka kudade ga rundunar yaki da ta'addanci a yankin kasashen Sahel sakamakon kara ta'azzarar harkokin tsaro.

EU AU Sahel Konferenz in Brüssel (Getty Images/AFP/O. Hoslet)

Taron kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin ninka kudade ga rundunar yaki da ta'addanci a yankin kasashen Sahel sakamakon kara ta'azzarar da harkokin tsaro ke ci gaba da yi. A bayyane take dai kasashen na Afirka kudu da hamadar Sahara na cikin dabaibayin matsalolin tsaro da karanci kudi da abinci gami da rashin jagoranci na kwarai.

Galibi ana danganta rashin tsaron da ke yaduwa cikin kasashen da tsananin talauci, wanda ke sanya matasa daukar makamai, wasu kuma ke zama barazana ga kasashen Turai, saboda kutsawar da suke yi cikin kasashen ta karfin tsiya. Kungiyar ta Tarayyar Turai din ce kuwa ta farko wajen yi wa rundunar ta G5 Sahel alkawarin euro miliyan 50 a bara, don ganin kasahen sun kaiga murkushe ayyukan tarzoma a yankin.