Tarayyar Turai ta nemi rarraba bakin haure | Labarai | DW | 27.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai ta nemi rarraba bakin haure

Kungiyar Tarayyar Turai ta nemi sake tsugunar da bakin haure tsakanin kasashe mambobi

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci kasashe mambobi kan karbar bakin haure kimanin 40,000 nan da shekaru biyu masu zuwa wadanda suka fito daga kasashen Siriya da Eritrea wadanda suka samu isa Italiya da Girka.

Kwamishinan kula da harkokin cikin gida na kungiyar Dimitris Avramopoulos ya bayyana haka yayin taron manema labarai a birnin Brussels na kasar Belgium. Dubban bakin haure daga wuraren da ake fama da yake-yake gami da masu neman samun kekkyawar rayuwa suke daukar kasadar tsallaka teku domin shiga kasashen Turai, inda wasu lokuta ake samun kifewar kananan jiragen ruwan da mutuwar mutane.