1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Takaddama kan magajin Juncker

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 29, 2019

A karshen watan Yuni mai zuwa ne kungiyar Tarayyar Turai EU, ke sa ran zabar sabon shugaban hukumar Tarayyar Turan wanda zai gaji shugabanta mai barin gado Jean-Claude Juncker.

https://p.dw.com/p/3JNm4
Europäische Kommission Eingang Personal
Hukumar Tarayyar Turai: Wa zai shige ta a matsayin sabon shugaba?Hoto: picture-alliance/Winfried Rothermel

A yayin taron kungiyar da ya gudana a ranar Talata, Merkel ta sake jadda goyon bayanta ga dan takarar jam'iyyar CSU Manfred Weber da ke neman zamowa magajin Junker. Sai dai rahotannin sun nunar da cewa shugaban Faransa Emmanuel Macron da wasu shugabannin kasashen kungiyar ta EU sun nuna adawarsu ga zabin nata, domin kuwa ba sa goyon bayan Weber. Merkel dai ta bayyana cewa shugaban majalisar Tarayyar Turan Donald Tusk zai yi wata ganawa da mambobin majalisar Tarayyar Turan da kuma shugabannin kasashen kungiyar ta EU a nan gaba.