Tarayyar Turai na matuƙar damuwa da rikicin Kyrgystan | Labarai | DW | 07.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai na matuƙar damuwa da rikicin Kyrgystan

Kantomar kula da harkokin waje na ƙungiyar tarayyar Turai ta buƙaci warware rigimar Kyrgystan cikin lumana

default

Kantomar kula da harkokin wajen tarayyar turai Catherin Ashton, ta bayyana damuwarta dangane da rikicin siyasar da ya ɓarke a ƙasar Kyrgystan, inda ta buƙaci gwamnati da kuma jam'iyyun adawar ƙasar da su bi lamarin sannu - a hankali. Mrs Ashton, ta buƙaci sassan biyu da su koma ga tattaunawa da nufin warware taƙaddamar dake tsakanin su, domin kaucewa ci gaba da zubar da jin.

Zanga - zangar adawa da mulkin shugaban ƙasar Kurmanbek Bakiyev dai, ta haddasa zubar da jini a yau Laraba, yayin da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka buɗe - wuta akan masu zanga zangar, kana wasu rahotannin da ba'a tabbatar da su ba na cewar, tuni aka kashe ministan kula da harkokin cikin gida na ƙasar. Hakanan, aƙalla mutane 17 ne suka rasu sakamakon taho - mu - gama a tsakanin sassan dake jayayyar.

Tashe - tashen hankular dai sun biyo bayan ziyarar da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya kai a ƙasar, inda 'yan jarida da kuma ƙungiyoyin farar hula suka fara jerin gwanon nuna adawa da rufe wata tashar Telebijin - mai zaman kanta, da kuma wata jarida.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita: Umaru Aliyu