1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Fara yi wa yara riga-kafin corona a EU

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 25, 2021

Hukumar Kula da Ingancin Magunguna ta Tarayyar Turai EU, ta bayar da damar yi wa yara da shekarunsu ya kama daga biyar zuwa 11 allurar riga-kafi samfurin BioNTech da Pfizer.

https://p.dw.com/p/43TTg
USA | Pfizer-BioNTech Covid-19 Impfung für Kinder
An jima da fara yi wa yara riga-kafin corona a Amirka da wasu kasashenHoto: Mike Blake/REUTERS

Sai dai kuma ba za a fara yin allurar ga yaran ba, har sai Hukumar Kungiyar Tarayyar Turan ta amince da shawarar. Wannan dai shi ne karon farko da kungiyar Tarayyar Turai za ta amince da yi wa yara 'yan kasa da shekaru 11 allurar riga-kafin corona, inda a baya ake yi wa 'yan shekaru 12 zuwa sama kadai.