1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Taraba: An nemi tsawaita zaman jami'an tsaro

July 7, 2017

Mukaddashi shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya tattauna da gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku kan rikicin Mambila inda gwamnatin jihar ta nemi tsawaita jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/2gAmT
Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Farfesa Yemi Osinbajo dai ya yi wannan zantawa da gwamnan na Taraba ne a fadar mulki ta Aso Rock da ke Abuja inda suka yi musayar yawu kan rikicin da ya yi sanadin hallakar mutane da kuma jawo asarar dukiya a karamar hukumar Sardauna da ke jihar ta Taraba. Gabannin wannan ganawa dai ministan cikin gidan kasar Janar Abdurahman Bello Dambazau da ya kai ziyara zuwa yankin a madadin gwamnatin tarayya ya mika rahoton binciken da suka gudanar kan wannan batu.

Jim kadan bayan kammala tattaunawa da mukaddashin shugaban kasar, gwamnan na Taraba ya zanta da manema labarai ciki kuwa har da wakilin DW Ubale Musa inda ya yi musu karin haske kan zaman da suka yi. Daga cikin irin abubuwan da suka tabo har da batun kara jami'an tsaro a Mambila da kuma irin yunkurin da gwamnatin jihar ke yi wajen ganin lamura sun daidaita kana gwamnan ya mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya saboda irin gudumawar da ta bada wajen ganin wutar rikicin ta mutu.

Du da cewar gwamnatin ta Taraba ta ce, ta na bakin kokarinta wajen ganin hankula sun kwanta, wasu kungiyoyi a jihar na cigaba da zargin gwamnati da hannu a wannan rikici sai dai gwamnatin jihar ta fito ta musanta wannan zargi da ake yi mata, har ma gwamnan ya ce ai hakkinsu ne su kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu don haka ba zai yiwu a ce su da kansu sun kunna wutar rikici ba.