Tanzaniya: Dalibai sun rasa rayukansu | Labarai | DW | 06.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tanzaniya: Dalibai sun rasa rayukansu

Rahotanni daga Tanzaniya na cewar yawan wadanda suka rasu sakamakon hadarin da wata mota kirar safa ta yi a arewacin kasar ya kai kimanin 32 yayin da wasu da suka jikkata ke cikin mawuyacin hali.

Wadanda wannan hadarin ya rutsa da su dai dalibai ne da shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 13 da malamansu biyu lokacin da suke wata ziyara a yankin nan na Arusha da akan je don yawon bude idanu. jami'an tsaro a Tanzaniya din suka ce hadarin ya auku ne lokacin da motar daliban ke saukowa daga wani tsauni inda ta fada cikin wani kogi. Yanzu haka dai jami'an sun ce suna gudanar da bincike don gano musababbin aukuwar wannan hadari.