Tanzaniya: An dakatar da gangamin adawa | Labarai | DW | 02.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tanzaniya: An dakatar da gangamin adawa

Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta dakatar da gangamin yakin neman zaben madugun adawa Tundu Lissu har tsawon kwanaki bakwai bisa karya ka'idojin kamfen na amfani da kalman da basu kamata ba.

Lissu wanda bai dade da koma wa kasar ba daga jinyar da ya kwashe shekaru uku a kasar Belgium bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani harin bindiga da aka kai masa a 2017, gangamin na daukar hankulan 'yan kasar.

A sanarwar da ta fidda hukumar zaben kasar ta ce an sami Mr Lissu da yada labaran bogi a kan shugaban kasar John Magufuli wanda ya ce yana yunkurin yin magudi a zaben da ke tafe.