1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantance makamai a Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa SB/USU
April 11, 2023

A Jamhuriyar Nijar ma'aikatar cikin gida ta fara aikin rijista da yin lamba ga bindigogin da fararen hula suka mallaka a cikin kasar domin sanin adadin makaman.

https://p.dw.com/p/4Pubk
Makamai a kasashen Afirka
MakamaiHoto: AP

A Jamhuriyar Nijar ma'aikatar cikin gida ta fara aikin rijista da yin lamba ga bindigogi mallakar farar hula a kasar. Makasudin wannan aiki wanda kamfanin SONIMA, wani kamfanin kasar mai kula da tantance bindigo ke tafiyar da shi, shi ne kiddiddige adadin bindigogin da fararan hula suka mallaka a kasar a bisa izinin hukuma, a wani yinkuri na samar da girgam ko rijista na bindigogin da ke da akwai a kasar. Shirin na da burin taimakawa ga shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.

Gwamnati ta kaddamar da wannan aiki ne na rijista da yin lamba ga bindigogi na fararan hula ne a karkashin wani shiri da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta bijiro da shi wanda ya tanadi kididdige bindigogin da fararan hula suka mallaka a yankin, a wani mataki na neman shawo kan matsalar yaduwar kananan makamai a tsakanin al'umma lokacin da matsalar tsaro ke addabar kasashen yankin da dama.

Yanzu haka dai tarin mutane farar hula da suka mallaki bindiga ne daya ko fiye sun fara zuwa kamfanin na SONIMA domin rijista da kuma yi wa bindigogin lamba. Tuni kungiyar masu sayar da bindogogi a Jamhuriyar Nijar ta bakin shugabanta Malam Moussa Ahmed ta bayyana gamsuwa da matakin gwamnatin. Ko baya ga birnin Yamai dai a nan gaba kamfanin na SONIMA ya sanar da shirin zuwa nan ba da jimawa ba sauran jihohin kasar domin kaddamar da wannan kamfe na yi wa bindigogin lamba.