Tantance dalilan mutuwar Arafat | Labarai | DW | 27.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tantance dalilan mutuwar Arafat

Ƙwararru za suyi nazari ko guba ce ta janyo mutuwar tsohon shugaban Falasɗinawa, bayan tono gawarsa.

A wannan Talatar ce ƙwararru na ƙasa da ƙasa za su binciki gawar tsohon jagorar Falasɗinawa marigayi Yesser Arafat domin tantance ko guba ce sanadiyyar mutuwar sa - kamar yadda galibin Falasɗinawa suka yi amanna. Ƙwararrun dai sun fito ne daga ƙasashen Switzerland, da Faransa da kuma Rasha.

A dai shekara ta 2004 ne Arafat ya mutu a birnin Paris na ƙasar Faransa yana da shekaru 75 a duniya sakamakon rashin lafiyar da aka dasawa ayoyin tambayoyi masu yawa.

Faransa ta ƙaddamar da bincike game da matsalar ce bayan da wasu ƙwararru daga ƙasar Switzerland suka gano sanadaran gubar polonium a jikin wasu daga cikin abubuwan daya ke anfani da su. Wasu Falasɗinawa na nuna yatsa ga Isra'ila, wadda ta yi masa ɗaurin ta'la'la a shekarun daya yi gabannin mutuwar ta sa, zargin da kuma ita isra'ila ta musanta. Arafat ya kasance shugaban Falasɗinu na farko tun a shekara ta 1996 har ya zuwa lokacin mutuwar sa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu