Tankar mai ta hallaka mutane a Najeriya | Labarai | DW | 01.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tankar mai ta hallaka mutane a Najeriya

Akalla mutane 70 ne aka bada labarin rasuwarsu bayan da wata tanka makare da man fetur ta fadi a birnin Onitsha da ke jihar Anambra a kudu maso gabashin kasar.

Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta ce baya ga wanda suka rasu, wasu da dama sun jikka sakamakon kunar da suka samu yayin da lamarin ya auku.

Wani jami'i Red Cross a jihar ya ce ta hanyar gwajin kwayoyin hallita na DNA ne kawai za a iya gane wanda suka rasu don kuwa gawarwakin sun kone kurmus.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda jihar ta Anambra ya ce hadarin ya auku ne bayan da kan motar ya kwace sanadiyyar gudun wuce sa'a da direban ke yi.