1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saka lokacin bayyana zaben Kwango

Suleiman Babayo
January 9, 2019

Karfe 11 na dare agogon Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango za a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar mai cike da rudani inda jami'an tsaro suka killace hukumar.

https://p.dw.com/p/3BHLr
DR Kongo Pressekonferenz der Wahlkommission
Hoto: DW/Wendy Bashi


Hukumar zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta ba da tabbacin wallafa sakamakon zaben shugaban kasa a wannan Laraba, yayin da ake ci gaba da zaman tararradi, bayan zargi tafka magudi. Mai magana da yawun hukumar ta ce ana shirye-shiryen karshe na ayyana sakamakon zaben saboda komai ya kammala kuma zuwa karshe 11 agogon kasar za a bayyana mutumin da ya samu nasara.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun killace hukumar zaben. Kowanne lokaci za su bayyana sakamakaon zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 30 ga watan jiya na Disamba a wannan dirkekiyar kasa da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka, lamarin da ke zama karo na farko za a mika mulki cikin kwanciyar hankali a kusan shekaru 60 da suka gabata a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda Shugaba Joseph Kabila da ya kwashe shekaru 18 kan madafun iko wa'adinsa ya kare tun shekaru biyu da suka gabata.

Akwai manyan 'yan takara uku da suke fata kan samun madafun ikon kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da suka hada da Emmanuel Ramazani Shadary mai samun goyon bayan gwamnati, sai kuma hamshakin dan kasuwa Martin Fayulu da Felix Tshisekedi na babbar jam'iyyar adawa.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu gami da takwaransa Edgar Lungu na Zambiya sun bukaci ganin wallafa sakamakon zaben domin kawo karshen zaman zullumi. Tuni kungiyoyin fararen hula suka bukaci jama'a su kasance cikin shirin zanga-zanga muddun sakamakon bai nuna zabin mutane ba.