tana kasa tana dabo a game da rikicin Israela da Hizboullah | Labarai | DW | 15.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

tana kasa tana dabo a game da rikicin Israela da Hizboullah

Rahotanni daga yankin gabas ta tsakiya na nuni da cewa har yanzu daftarin sulhun da Mdd ta zartar a game da kawo karshen rikicin Israela da kungiyyar Hizbollah na nan na aiki yadda yakamata.

To sai dai kuma a lokacin da sakataren Mdd, Kofi Anan yake bayyana jin dadin sa na ganin cewa, daftarin sulhun ya fara aiki,

kafafen yada labaru sun rawaito dakarun sojin Israela na fadin cewa, koda a daren jiya , sai da yan kungiyyar Hizboullah suka harba musu rokoki, to amma babu daya daya dira a iyakar kasar , ballantana ya jiwa wani rauni.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin yan gudun hijira na Kasar Lebanon sun fara dawowa izuwa gida, bayan da al´amurra suka fara lafawa.

A hannu daya kuwa, kungiyyar bayar da tallafin gaggawa ta kasa da kasa, wato Red Cross tace har yanzu akwai bukatar ci gaba da gudanar da ayyukan bayar da agaji bisa irin matsanancin hali da da yawa daga cikin mutanen kasar suka shiga, a sakamakon wannan rikici.