Tallafin Turai kan wanzar da zaman lafiya | Labarai | DW | 09.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tallafin Turai kan wanzar da zaman lafiya

Jakadar Amirka da ke zauren Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta bukaci kasahen Turai da su fadada gudumawar su wajen aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya.

Ms. Power ta ambata hakan ne a birnin Brussels na kasar Belgiyum a cigaba da ziyarar da ta kaita kasar inda ta ke cewar wannan shi ne lokacin da ake bukatar karin tallafin Turai wajen aiyyukan wanzar da zaman lafiya duba da irin kwarewar da suke da ita da kuma kayan aiki irin na zamani.

Jakadar ta Amirka ta ce a shekaru 20 da suka gabata Turai ta fi kowacce nahiya yawan dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya to sai dai a yanzu hakan ya ja baya sosai.

Amirka dai yanzu ita ce ke kan gaba wajen yawan soji da ke irin wannan aiki musamman ma karkashin inuwar kungiyar tsaro ta NATO amma matsi na tattalin arziki ya sanyata neman agaji daga sassan duniya.