Tallafin makamai ga ′yan tawayen Siriya | NRS-Import | DW | 18.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Tallafin makamai ga 'yan tawayen Siriya

NATO ta ce ba za ta tsoma baki a muhawar da EU ke yi na baiwa 'yan tawayen Siriya makamai ba.

Sakatare janar na kungiyar kawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen, ya fadi a wannan Litinin cewar, kungiyar ba ta da niyyar jefa kanta cikin muhawar da kungiyar tarayyar Turai ke yi game da batun samar da makamai ga 'yan tawayen Siriya. Ya ce batun dai ya shafi kungiyar tarayyar Turai ne kawai, kuma ba shi da wata anniyar sanya baki a ciki.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Asabar da ta gabata ce kantomar kula da manufofin ketare a kungiyar Catherin Ashton, ta yi gargadin bin lamarin cikin tsanaki bisa shawarar da kasashen Faransa da Birtaniya suka gabatar ta neman a baiwa 'yan tawayen da ke yakar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad makamai, tana mai cewar tilas ne shugabannin kungiyar su yi nazarin abinda ka iya zuwa ya koma idan har sun dauki matakin.

Shi kuwa sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry, cewa yayi gwamnatin shugaba Obama ba ta adawa da matakin da wasu kasashen na Turai za su dauka na samar da makamai ga 'yan tawayen na Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar