TALLAFI GA MASU CUTAR AIDS | Siyasa | DW | 24.11.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TALLAFI GA MASU CUTAR AIDS

A halin yanzu dai, kasar Afrika Ta Kudu ta yanke shawara akan samarwa jama'ar wannan kasar da suka kamu da cutar HIV/AIDS magani kyauta a duk fadin kasar. A baya dai kasar tayita jan kafa na tsawon shekaru 5, akan daukar matakin.

To a halin yanzu, daga nan zuwa shekaru 5 masu zuwa, dai, ana saran mutane fiye da miliyan, da suke fama da wannan cutar ne, zasu kasance suna samun wannan maganin kyauta a cikin kasar Afrika Ta kudun. Ita kanta gwamnatin, a halin yanzu zata samu saukin daukar nauyin bayar da maganin AIDS din kyauta, saboda, kudin maganin yayi sauki,a bisa kasancewar sa, kasa, da lunki 50, akan yadda kudin sa, suke a watan Nuwamba na shekara ta 2002, a bara kenan i warhaka. Wannan raguwar kudin magamnin kuwa, ya biyo bayan kamfe din da ake tayi ne, a duniya, akan a rage tsadar maganin, domin taimakawa jama'ar dake fama da wannan cutar, data addabi jama'a a duniya, musanman ma,a kasashe, da dama, a cikin Nahiyar Afrika. Kamfanonin magungunan da suka ji wadannan kiraye kirayen ne, suka amince da saukar da farashi akan magungunan, a halin da ake ciki. Wannan na cikin nasarar da tasa kasar Afrika Ta Kudun, ta shiga bada magungunan kyauta yanzu ga jama'ar kasar ta, da suka kamu da wamnnan cutar,ita kuma take daukar nauyin sawo wadannan magungunan, wanda, daba hakan ba, da kuwa, yanada, wuya, kasar ta iya daukar nauyin, saye da rarraba magungunann kyautar. Ministan Lafiya na kasar Manto Tshabalala-Msimang, yace yanzu haka, kasar Afrika ta Kudun, na cikin kawance da kamfanonin magunguna, a cikin nasara, ta yadda wannan aikin ba zai samu wani cikas ba. Sannan kuma, kasar na yunkurawa, wajen sarrafa magungunan, a cikin gida. Babban jami'in hukumar kula da cutar HIV/AIDS, na majalisar dinkin duniya,Peter Piot, dai, ganin wannan hobbasar da kasar Afrika Ta Kudu, tayi, abun yabo, kamar yadda ya bayyana, yace, akwai bukatar a shawo kan sauran kasashen dake cikin Nahiyar Afrika, wadanda jama'ar su ke fama da wannan cutar, da suma, su dauki irin matakin da Afrika Ta Kudun ta dauka, na daukar nauyin,bayarda magungunan cutar AIDS kyauta, ga jama'arsu. Yace ta wannan hanyar, da kasar, ta Afrika Ta Kudu ta dauke,ne, za'a iya samun cin nasarar yaki da cutar HIV/AIDS, a Nahiyar Afrika.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar Afrika Ta Kudun, sai shan yabo take tayi, daga kungiyoyin yaki da wannan cutar na kasar da kuma kungiyoyin kwadago na wannan kasa, akan daukar wannan matakin. Shugaban wata kungiya mai zaman kanta, a kasar akan harkokin kula da wadanda suka kamu da cutar HIV/AIDS din,Nkululeke Nxesi, ga misali, ya bayyana gamsuwar sa,yana mai cewar, wannan abun kawo masu halin dan-dan-dan-dan ne, muddin dai,an aiwatar da wannan tsarin, wanda yake ganin zai taimakawa mutane masu dama, a wannan kasar.
Kasar Afrika Ta Kudu dai, itace kasar da tafi sauran kasashen duniya yawan wadanda suke dauke da kwayoyin cutar HIV mai haddasa cutar AIDS din, kamar yadda wani kiyasi na majalisar dinkin duniya, ya nunar. Domin akwai masu dauke da cutar, miliyan 5, a cikin jama'ar kasar su miliyan 45. Sannan kuma, cutar a halin yanzu, itace kan gaba, wajen daukar rayukan jama'ar kasar, a cikin abubuwan dake zama sanadin rasa, rayuka a wannan kasar, kamar yadda binciken cibiyar Lafiyar kasar, dake da manyan ofisoshin ta, a Pretoria da Cape Town da a Durban, ya nunar. Gwamnatin kasar Afrika Ta Kudun dai, zata kashe kudi fiye da dola miliyan 45 a cikin shekarar farko, ta aikin aiwatar da wannan shirin, sannan zata kashe kudi dola biliyan 1 da rabi, a cikin shekaru biyar, din, da aka ware a cikin aikin samarda magungunguna kyauta, akan cutar AIDS, tare da ayyukan inganta cibiyoyin samar da lafiya.

 • Kwanan wata 24.11.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D: MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvnU
 • Kwanan wata 24.11.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D: MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvnU