Tallafawa al′umma a kewayen tafkin Chadi | Labarai | DW | 28.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tallafawa al'umma a kewayen tafkin Chadi

Babban jami'in da ke kula da ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Duniya Stephen Obrien ya nemi da a agaza wa al'umma a wasu yankuna na Najeriya da Tafkin Chadi.

Stephen OBrien PK UN

Stephen Obrien mai kula da fannin agajin gaggawa a Majalisar Dinkin Duniya

A cewar babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ma kula da agajin gaggawa, dubabban al'umma ne ke cikin mawuyacin hali amma kuma ana mantawa da su. Mista Obrien ya jaddada wannan kira ne a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya yi kira ga kasashe da sauran masu hannu da shuni da su bada tasu gudunmawa cikin gaggawa. A kalla dai mutane miliyan tara ne ke cikin bukatar agaji a wadannan yankuna na arewa maso gabashin Najeriya da kuma kewayen tafkin Chadi.