Tallafa wa yara marayu a makarantu a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 28.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Tallafa wa yara marayu a makarantu a Najeriya

Wani matashi dan shekaru 20 da haihuwa a karamar hukumar Dutsi da ke jihar katsina ya sha alwashin sadaukar da kansa wajen tallafama Dalibai.

A karan farko matashin ya je makarantu 20 ya lalubo yara marayu da marasa galihu akalla 525 ya dinka musu kayan makaranta.Kalubalen da marayu da marasa galihu ke fuskanta a makarantun wadan nan yanki na daya daga cikin dalilan ba da  wannan taimako da  matashi Ibrahim Abubakar Sirika ya ke yi ga kuma abin da ya kara da cewar:
"Abin da ya sa na yi kokarin ba da kayan makaranta 'yan makaranta marayu shi ne na ba su himma  domin su dage suma su yi karatu su ji dadin shiga tsararrakinsu su samu natsuwa domin ci gaba da yin karatu don samun makoma ta gari a gobe.''

 

Sauti da bidiyo akan labarin