Taliban sun kashe dan uwan ma′aikacin DW | Labarai | DW | 20.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taliban sun kashe dan uwan ma'aikacin DW

Mayakan Taliban sun harbe daya daga cikin dangin wani dan jaridar tashar Deutsche Welle tare da yi wa wani dan uwansa mummunan rauni a lokacin da suka kaddamar da farmakin neman dan jaridar.

 

Yan Taliban din dai sun dade suna neman dan Jaridar na tashar DW wanda a yanzu yake aiki daga nan Jamus. Sauran danginsa sun tsere inda a yanzu suke buya.

Shugaban tashar DW Peter Limbourg ya yi Allah wadai da harin inda ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Jamus ta dauki mataki. Yace kisan da yan Taliban suka yi wa wani dangi na daya daga cikin editocin mu abin daga hankali ne kwarai wanda ya nuna irin halin da ma'aikatan mu da kuma iyalansu suke fuskanta a Afghanistan.

A halin da ake ciki 'yan Taliban din suna bi gida-gida suna farautar yan Jarida a Kabul da sauran gundumomi.